Bayan SSANU Da NASU, Wata Kungiyar Ma'aikatan Jami'a Ta Janye Yajin Aiki

Bayan SSANU Da NASU, Wata Kungiyar Ma'aikatan Jami'a Ta Janye Yajin Aiki

  • Kungiyar ma'aikatan fasahar da ke jami'o'in Najeriya (NAAT) ta dakatar da yajin aikinta na kimanin wata shida
  • Ibeji Nwokoma, shugaban NAAT na kasa ya ce sun dakatar da yajin aikin ne na wata biyu don bawa gwamnati daman aiwatar da yarjejeniyarsu
  • Yayin da kungiyar ta ce umurci ma'aikata su koma bakin aiki, ta fada wa gwamnati ba za ta amince da dokar 'ba aiki, ba kudi ba'

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Kungiyar Ma'ikatan Fasahar da ke a Jami’o’in Najeriya, NAAT, ta dakatar da yajin aikin da take yi na tsawon wata biyar a fadin kasa, Daily Nigerian ta rahoto.

Shugaban NAAT na kasa, Ibeji Nwokoma, wanda ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a Abuja, ranar Alhamis ya ce dakatarwar kawai na wata uku ne.

Kara karanta wannan

N9.7trn: A Yi Amfani Da 'Kudin Abacha' Don Warware Matsalar ASUU, In Ji Dan Majalisar Najeriya

Mambobin NAAT
Bayan SSANU Da NASU, Wata Kungiyar Ma'aikatan Jami'a Ta Janye Yajin Aiki. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai ta ce ba ta amince da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’ ba na gwamnatin Najeriya ba.

Nwokoma ya ce sun yi zaben raba gardama kuma kashi 80 cikin 100 sun goyi bayan dakatar da yajin aikin yayin da kashi 19 suka ce a cigaba.

Shugaban na NAAT ya ce yayin yajin aikin, kungiyar ta yi taruruka da wakilan gwamnatin tarayya, ciki har da ministan kwadago da samar da ayyuka, Dakta Chris Ngige.

Ya ce kungiyar, bayan tattaunawar da gwamnati sun yi nasarar cimma matsaya kan wasu bukatunsu, duk da cewa ba su amince da tsarin 'ba aiki, ba biyan albashi' na gwamnatin tarayya ba.

Ya lissafa abubuwan da gwamnatin ta amince da su har da fitar da takardar da ke bada damar aiwatar da CONTISS 14 da 15 ga masana fasahar ilimi da biyan basusukan kudaden alawus-alawus da wasu abubuwan.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Shehin Malami a Yobe

NAAT ta umurci dalibai na ajin karshe da ke bincike a dakin gwaji su dawo makaranta

Sakamakon hakan, NAAT ta umurci daliban ajin karshe da wasunsu da ke bincike da wasu ayyukan gwaje-gwaje su dawo makaranta su kammala aikinsu.

Ba mu yarda da tsarin 'ba aiki, ba albashi ba'

Ya ce ba su amince da matakin gwamnatin na 'ba aiki, ba albashi ba' yana mai cewa ba kungiyar bane ta janyo yajin aikin, gwamnati ne ta ki biya musu bukatunsu kan lokaci.

"Ya kamata a lura cewa NAAT ta bi dukkan ka'idoji kafin fara yajin aiki, don haka, NAAT na kira da kakkausan murya a biya mambobinta dukkan albashinsu da aka rike ba tare da bata lokaci ba."

SSANU Da NASU Sun Janye Yajin Aiki, Amma Sun Saka Wa Gwamnatin Tarayya Sharadi

Tunda farko, kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, SSANU da na kungiyar ma’aikatan jami’o’i NASU, a ranar Asabar, sun dakatar da yajin aikinsu bayan gajeren zama da suka yi da ministan Ilimi, Adamu Adamu a Abuja.

Kara karanta wannan

Mu ma mutane ne: Ma'aikatan wata jiha sun fito zanga-zangan rashin biyansu albashi na shekaru 5

Ana sa ran janyewar zai fara aiki ne daga ranar Laraba na mako mai zuwa, Channels TV ta rahoto.

A cewar ministan ilimin, gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 50 don biyan allawus na mambobin SSANU da NASU da na Kungiyar ASUU.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164