Kungiyar Izalah Ta Bayyana Abinda Zatayi Da Kudin Fatun Layya N107m Da Ta Samu

Kungiyar Izalah Ta Bayyana Abinda Zatayi Da Kudin Fatun Layya N107m Da Ta Samu

  • Kwana daya bayan bayyana adadin kudin fatun layya da aka samu, Izalah ta bayyana abinda za'ayi da kudin
  • A kowace shekara, kungiyar addinin na tara fatun layya na sadaka daga wajen jama'a ana ayyukan kungiyar da su
  • Bayan gina Masallaci a Abuja da akayi da kudin wanda Shugaba Buhari ya kaddamar, yanzu za'a zuba kudin wajen ginin jami'a

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kungiyar addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqaamatus Sunnah watau JIBWIS ta bayyana abinda za'a yi da kudin fatun layyan da aka samu jiha bana.

Mun kawo muku jiya cewa Izalah ta alanta samun naira miliyan dari da bakwai (₦107,704,484.25) na tattara fatun layyan shekarar 1443AH.

A baya an gina katafaren masallaci, gidan shan magani da katafaren masaukin baki a cikin birnin Abuja duk da kudaden fatun layyan da jama'a ke badawa, kungiyar ta bayyana.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikicin addini ya barke tsakanin kirista da 'yan gargajiya, an kashe wani

Yanzu kungiyar tace za'a zuba kudaden ne wajen ginin Jami'ar kasa da kasa ta As-Salam dake jihar Jigawa.

A jawabin da ta saki ranar Alhamis, JIBWIS tace wannan karon ginin Jami'a za'a yi da kudin.

JIBWIS tace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kamar dai yadda aka gani an gabatar da ayyukan alkhairi da kudin fatun layyar da kudin rasidai da yan'uwa ke badawa wanda daga ciki aka gina masaukin baki na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a Abuja, Babban Masallacin Juma’a a Helkwatar JIBWIS a Abuja inda yanzu kuma za’a shigar da kudin a gagarumin aikin gina Jami’ar As-Salam dake garin Hadejia Jihar Jigawa."
As Salam
Kungiyar Izalah Ta Bayyana Abinda Zatayi Da Kudin Fatun Layya N107m Da Ta Samu Hoto: JIBWIS
Asali: UGC

Jerin Adadin Kudin Fatun Layyan Da Izalah Ta Samu Daga Kowace Jiha, Sakkwatawa Ne a Gaba

Kungiyar JIBWIS ta bayyana filla-filla adadin kudin fatun layyan da aka samu daga kowace jiha bana.

Jihar Sakkwato ce tafi bada gudunmuwa na fatun layya, sannan jihar Kaduna, sai kuma jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Iyayen Dalibai Za Su Fara Yi Wa Gwamnatin Tarayya Karo-Karo Na N10,000

Duba jadawalin nan

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida