Sanatocin APC 15 cikin 17 Masu Niyyar Sauya Sheka Sun Yanke Shawara

Sanatocin APC 15 cikin 17 Masu Niyyar Sauya Sheka Sun Yanke Shawara

  • Akalla Sanatocin jam'iyyar APC 15 cikin 17 masu niyyar sauya sheka sun yanke shawarar cigaba da zama a APC
  • Sanatocin sun ce zasu cigaba da zama a APC maimakon komawa PDP sakamakon alkawarin da Shugaba Buhari ya yi
  • Bayanai sun nuna cewa an yi wa wadannan Sanatoci alkawarin wasu mukamai masu tsoka idan Tinubu yayi nasara

FCT, Abuja - Sakamakon sa bakin Shugaba Muhammadu Buhari, Sanatoci 15 cikin 17 da ke niyyar fita daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun sauya shawara, sun fasa fita.

The Nation ta ruwaito cewa Sanatocin a baya sun nuna bacin ransu kan sakamakon zabukan fidda gwanin da aka gudanar watannin baya.

Yanzu sunce sun hakura da sauya sheka kuma zasu cigaba da zama a jam'iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

Legit.ng ta tattaro cewa an yiwa wadannan Sanatoci alkawarin wasu mukamai masu tsoka idan APC tayi nasara a zaben shugaban kasa.

Daya daga cikin Sanatocin yace:

"Bisa alkawuran da Shugaba Buhari yayi mana da wasu shugabannin jam'iyyar, mun yanke shawarar cigaba da zama a jam'iyyar yayinda zamu sa ido kan ganin yadda za'a biya bukatunmu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Alkawarin da akayi mana yanzu shine za'a bamu mukamai idan jam'iyya ta lashe zabe a 2023. Duk da haka, babu wani matakin cika alkawarin da suka dauka."

Wannan na nuna cewa jam'iyyar APC za ta cigaba da zama mai rinjaye a Majalisar dattawa

Senate
Sanatocin APC 15 cikin 17 Masu Niyyar Sauya Sheka Sun Yanke Shawara Hoto: NGRSenate
Asali: UGC

.

Bamu Yarda Ba, Sai Mun Fita Daga APC: Sanatoci Biyu

Majiyoyi da TheNation ta nakalto sun bayyana cewa mutum biyu cikin Sanatoci 17 sun ce tuni sun yanke shawara, ba zasu cigaba da zama a APC ba.

Kara karanta wannan

Muna Son Lashe Zaben Akalla Jihohi 25 a Zaben 2023 Kamar Yadda Muka Saba, Shugaban PDP Iyorchia Ayu

Wani Sanata yace:

"Kawo yanzu, Sanatoci biyu kadai cikin suka ce zasu fita kuma babu ruwansu da harkokin jam'iyyar."

2023: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Jerin ‘Yan Takaran da Buhari Zai Marawa Baya

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sai ‘yan takaran da jam’iyyar APC ta tsaida kadai zai taya kamfe a zabe mai zuwa na 2023.

The Nation ta rahoto Garba Shehu yana cewa babu ruwan Mai girma Muhammadu Buhari da tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya-sheka.

Kamar yadda Malam Shehu ya fada a jawabin da ya fitar a ranar Laraba, shugaban kasar ba zai taya wadanda suka kai APC kotu wajen kamfe ba.

Hadimin shugaban kasar yace Mai gidansa ba zai ci amanar jam’iyyarsa ta APC a zaben badi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida