Muna Son Lashe Zaben Jihohi 25 a Zaben 2023, Shugaban PDP Iyorchia Ayu
- Uwar Jam'iyyar PDP ta tattara yan takararta a birnin tarayya Abuja don tattaunawa da su a Abuja
- Shugaban jam'iyyar PDP yace suna son lashe zaben akalla jihohi 25 a zaben 2023 kamar yadda suka saba
- Har Ila Yau ana cigaba da sa'insatsakanin dan takarar shugaban kasa jam'iyyar Atiku Abubakar da Nyesom Wike
Abuja - Shugaban Uwar Jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyanawa 'yayan jam'iyya cewa suna da tabbacin lashe zabe a jihohi 25 a zaben 2023.
Ayu yace a 2023, PDP zata dawo da mulkin jihohi da yawa kamar yadda ta saba zamanin Obasanjo da Jonathan.
Ya bayyana hakan ne bayan ganawar shugabannin jam'iyyar da yan takara kujerun gwamna ranar Laraba a hedkwatar jam'iyyar dake Abuja, rahoton Punch.
A cewar Ayu, yan takaran sun gana da mambobin kwamitin don jin abubuwan da suke yi don nasara a zabe a jihohinsu.
Yace:
"Yan takaran sun zo kuma sun bayyana halin da ake ciki a jihohinsu. Sun sanar da mu kan kokarin da sukeyi don nasara a zabe."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Muna son nasara a jihohi 25 kamar yadda muka saba."
"Muna son nasara a tarayya, a jihohi, majalisar dokoki da kujerun gwamna."
Gwamna Bala na Bauchi, a karshen taron ya bayyana cewa yan takaran sun zauna ne don tattauna halin rikicin da jihar ke ciki.
Yace:
"Yan takaran sun hadu ne don hada kan jam'iyyar da kuma tattauna lamarin sulhu."
A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Sule Lamido
A wani labarin kuwa, tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wani laifi da aka yiwa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kuma a rabu da shi yayi abinda ya ga dama.
Lamido ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV
Yace jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na da kundin tsarin mulki da dokoki kuma zabe akeyi don zaben duk wani dan takara.
Asali: Legit.ng