'Yan Sanda Sun Cafke Yaro Mai Shekaru 9 Dake Tukin Ganganci Zuwa Makaranta Tare Da Mahaifinsa Da Yar’uwarsa

'Yan Sanda Sun Cafke Yaro Mai Shekaru 9 Dake Tukin Ganganci Zuwa Makaranta Tare Da Mahaifinsa Da Yar’uwarsa

  • An garkame wani dan shekara 40 a safiyar yau Laraba, 24 ga watan Agusta, bayan jami’an yan sanda sun ga karamin dansa yana tuka mota
  • Yaron mai shekaru tara yana tuki zuwa makaranta lokacin da yan doka suka gano shi, mahaifinsa na zaune a kujerar fasinja sannan kanwarsa na kujerar baya
  • Wanda ake zargin, wanda ya ikirarin cewa ya horar da dansa a harkar tuki, zai gurfana a gaban kotun Mavoko

Kenya – Jami’an yan sandan Machakos da ke kasar Kenya sun kama wata mota da karamin yaro dan shekaru tara ke tukawa a hanyar Mombasa.

Jami'an yan sandan Kenya
'Yan Sanda Sun Cafke Yaro Mai Shekaru 9 Dake Tukin Ganganci Zuwa Makaranta Tare Da Mahaifinsa Da Yar’uwarsa Hoto: NPS.
Asali: Facebook

Lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 24 ga watan Agusta, bayan jami’an yan sandan kan hanya sun gano karamin yaron sanye da kayan makaranta yana tuka motar yayin da mahaifinsa ke zaune a mazaunin fasinja nag aba sannan diyarsa na zaune a kujerar baya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4

A cewar wani rahoto daga jaridar Nation Africa, a lokacin da jami’an tsaron suka tsayar da motar, sai yaron ya tserewa yan dokar sannan ya kara gudu ta yankin Athi township.

Jami’an tsaron sun bibiyi motar sannan suka yi nasarar tsayar da ita yayin da take gab da shiga wata makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Jami’an yan sandanmu sun yi nasarar damke yaron kafin ya shiga makarantar. Yana tuki da gudu, cike da hatsari kuma bai sanya belit din direba ba,” in ji kwamandan Athi River Base.

Har yanzu mahaifin yaron mai shekaru 40 na tsare a ofishin yan sandan Athi River yayin da jami’an suka ajiye kanan yaran biyu a makaranta.

Ya ce yaronsa ya shafe kimanin shekaru biyu yana tuki bayan ya horar da shi a kan yadda ake tukin.

“Na san yana da hatsari amma ta faru,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an Yan Sanda Suka Je Har Wajen Shagalin Biki Suka Kama Amarya Kan Zargin Sata

Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun Mavoko, Standard Media ta rahoto.

Bidiyon Hazikin Dan Najeriya Yana Tallan Doya A Landan, Ya Ce Ya Tara N116k Cikin Awanni 4

A wani labarin, mun ji cewa duk a kokarin samun karin kudaden shigarsa, wani hazikin dan Najeriya ya fara tallan doya a unguwannin Landan.

A cikin wani bidiyo mai ban sha’awa, an gano mutumin tsaye a kan titi yana siyar da doyansa cike da alfahari da sana’arsa.

A cewar bidiyon, karin kudaden shigan zai taimaka masa wajen biyun haraji a Ingila inda yake da zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng