Wike Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Tafi Turai Ganawa da Tinubu Ranar Litinin, Majiya
- Yayinda zaman sulhu da Atiku yaci tura, gwamnan jihar Ribas ya garzaya Turai ganawa da Tinubu
- Wike ya samu rakiyar wasu takwarorinsa gwamnoni biyu dake goyon bayansa a rigimarsa da Atiku
- Gwamna Wike ya shiga adawa da Atiku ne bisa rashin zabensa matsayin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na PDP
Labarai sun bayyana cewa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya tafi nahiyar Turai ganawa da dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu.
TheCable ta ruwaito cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu da wasu manyan jigogin PDP na hallare a zaman.
Wike da tawagarsa sun tafi Turai ne da safiyar Litinin, 22 ga Agusta, 2022.
A riwayar Vanguard, ana hasashen wannan ganawa bai rasa alaka da goyon bayan Tinubu a zaben 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiyoyin suka ce,
"Wannan shine dalilin da yasa Gwamnan Nyesom Wike, wanda babban mamban kungiyar lauyoyi ne da dan takarar kujerar shugaban kasar APC, Bola Tinubu, basu halarci taron NBA ba da ya gudana a Legas."
Wannan ganawar na tabbatar da labarin cewa Nyesom Wike na ganawa da dan takarar APC, Bola Tinubu, tun kafin zaben fidda gwanin PDP."
Hakazalika wannan na nuna cewa WIke da mabiyansa na yaudarar zaman sulhun da akeyi ne saboda ya yanke shawarar illata PDP da dan takararta a 2023, Atiku Abubakar, daga baya su koma APC ko LP.
A cewar majiyar, Wike da mabiyansa na shawara kan wanda zasu goyi baya a zaben shugaban kasar 2023.
Kana an samu labarin cewa suna shirin ganawa da Peter Obi, dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Party.
Sulhun Atiku da Wike: Bayan Zaman Sa'o'i 4 Ranar Juma'a, Har Yanzu An Gaza Cimma Matsaya
Mambobin kwamitin sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike, sun sake zama.
Mambobin sun tattauna na tsawon sa'o'i hudu a birnin Fatakwal ranar Juma'a, 19 ga watan Agusta amma har yanzu abin ya ci tura, rahoton ThisDay.
Wike na cigaba da nuna adawarsa ga Atiku Abubakar bisa rashin zabensa matsayin abokin tafiya a tikitin takara.
Wanda ya jagoranci kwamitin sulhun kuma tsohon Gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, bayan zaman a bayyana cewa har yanzu da sauran rina a kaba kuma zasu yi sabon zama.
Asali: Legit.ng