Har Gobe Gidan Haya Nike a Abuja, Rokon Allah Nike Ya Bani Nawa: Shekarau

Har Gobe Gidan Haya Nike a Abuja, Rokon Allah Nike Ya Bani Nawa: Shekarau

  • Malam Shekarau ya bayyana cewa har yanzu bai mallaki gida ko guda a birnin tarayya Abuja ba
  • Shekarau ya ce ko kadan kudi bai taba rudarsa ba saboda haka aikin banza ne wani yayi masa sharrin kudi
  • Tsohon gwamnan jihar Kanon ya sanar da cewa Kwankwaso mayaudari ne kuma ya fita daga NNPP

Kano - Sanata Mai Wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya kuma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa har yanzu bai da gidan kansa a Abuja.

Shekarau, wanda tsohon Gwamnan jihar Kano ne tsawon shekaru takwas (2003-2011) ya bayyana hakan ne ga mabiyansa yayin martani kan zargin cewa an bashi kudi $1 million ya fita daga jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Wannan ya biyo bayan jawaban da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, yayi kan Malam Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Shekarau ya fito ya yi bayanin dalilan da suka ja ya bar NNPP ya raba gari da Kwankwaso

Shekarau
Har Gobe Gidan Haya Nike a Abuja, Rokon Allah Nike Ya Bani Nawa: Shekarau Hoto: Ibrahim Shekarau
Asali: Twitter

Shekarau yace duk shekarun da yayi a harkar siyasa, babu irin kudinda bai gani ba kuma yafi karfin wani ya bashi kudi don yayi wani abu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Har gobe, kuma ba fada nike don mutane su sani ba, gidan haya nike a Abuja. Addu'a nike Allah ya bani kudi in gina nawa."
"Babu irin kudin da hannuna bai bada approval (izinin fitarwa) ba. Ga kwamishanoni nan, ban taba a zaman majalisar zartaswa in ce lallai ga wanda za'a ba kwangila ba."
"Ko wa ya san darajar fili a Kano kuma akwai kwamishanonin filaye da dama a nan. Bayan gidan da gwamnati ta gina min cikin tsarin fansho, Ko kafa daya na fili bani da shi a Kano."

Shekarau ya kara da cewa ba wai kudi ne baya so ba, amma mutunci ya fi masa kudi.

Kara karanta wannan

Kai mayaudari ne: Shekarau ya dira kan Kwankwaso, ya fasa kwai kan maganar sauya sheka

Dalilin da yasa na fice daga NNPP, na raba kaina da tafiyar Kwankwaso

Bayan sauka da motar jam'iyyar NNPP mai alama kayan marmari, Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilan da suka sa yi watsi da jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Sheakau dai shi ne sanata mai wakiltar Kano tsakiya a majalisar dattawa, kuma ya fice daga APC bayan rasa tikitin komawa takara, inda ya koma NNPP aka bashi tikitin.

Shekarau ya bayyana cewa, yanke fice daga NNPP ne biyo bayan hana magoya bayansa foma-fomai tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel