Kasuwar Maza Inda Mata Ke Zuwa Sayan Mijin Aure a Kasar Indiiya
- Akwai wata kasuwa a kasar Indiya inda Maza ke tallata kansu ga Mata don su auresu
- A kasar Indiya, akwai wata tsohuwar al'ada inda Mata ke biyan kudin Sadakin Mazajen da zasu aura
Indiya - Labarin Wata kasuwa a kasar Indiya inda tuzurai ke taruwa a shekara suna sauraron matan da zasu sayesu don aure ya tayar da cece-kuce kafafen ra'ayi da sada zumunta.
Mata masu neman miji tare da iyayensu na zuwa kasuwan ne don zaben mijin da ya musu.
Ana sayen namiji bisa nasabar danginsa da kuma adadin karatun da yayi
Kasuwar Mazan na Madhubani, dake jihar Bihar kuma ana kiranta da suna Saurath Mela ko Sabhagachhi.
Mazan na taruwa karkashin bishiyoyi a kasuwar tsawon kwanaki tara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar masana tarihi, wannan kasuwa ya kwashe shekaru 700 yana ci kuma Shugaban Daular Karnat, Raja Hari Singh, ne ya kafa don taimakawa mata wajen samun mazan aure.
An ruwaito cewa matan sun fi son namijin da yayi karatu musamman Injiniya, Likita da ma'aikatan gwamnati.
Duk da gwamnatin Indiya ta haramtawa mata biyan kudin sadaki, har yanzu wannan al'ada na cigaba da gudana a kasar.
FIFA ta Hana Indiya Shiga Kwallo, An Kawo Hujjar Dakatar da Kasar a Duniya
A wani labarin, Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta Duniya ta dakatar da kungiyar All India Football Federation (AIFF), ba tare da wani bata lokaci ba.
Kamar yadda FIFA ta wallafa a shafinta na yanar gizo dazu, an dauki wannan mataki a kan kungiyar kwallon kafan ne saboda katsalandan.
Sanarwar da aka fitar a ranar Talata ta nuna akwai yiwuwar a dakatar da kungiyar kwallon kafa na mata, wanda zai iya kawowa Indiya cikas.
Asali: Legit.ng