Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi
- DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana yadda Sheikh Goni Aisami ya taimaki wanda bai sani ba a kan titin Nguru amma ya kare da halaka shi
- Sojan sanye da kayan gida ya tsayar da malamin tare da rokonsa da ya rage masa hanya, a kan hanyar ne malamin ya tsaya inda sojan yayi amfani da AK-47 wurin bindige shi
- Ya wurgar da gawar malamin amma ya kasa tserewa da motarsa, lamarin da yasa ya kira wani abokinsa wanda 'yan sa kai suka ritsa su a wurin
Yobe - An kara samun bayanai kan mutuwar Sheikh Goni Aisami, fitaccen malamin addinin Islama na Yobe jihar Yobe wanda aka bindige a ranar Juma'a.
Kamar yadda DSP Dungus Abdulkarim, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe ya bayyana, mutum biyun da ake zargi sojoji ne daga bataliya ta 241 sake Recce a Nguru sun shiga hannu.
Sunaye: An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe
Daily Trust ta rahoto cewa, yace lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan Aisami ya ragewa daya daga cikin wadanda ake zargin hanya.
Kakakin rundunar 'yan sandan yace Aisami na tuka motar daga Gashua zuwa Nguru, lokacin da wanda aka zargin ya tsayar da shi da kayan gida dauke da gado kuma ya roki malamin da ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A lokacin da suka kusa Jaji-Maji, malamin ya tsayar da motar domin biyan bukata," yace inda yana dawowa wanda ake zargin ya fito da Ak-47 ya bindige shi har sau biyu.
Abdulkarim ya kara da cewa, wanda ake zargin ya yi kokarin tserewa da motar mamacin amma ya kasa saboda makalewa da tayi a tabo kuma ta kasa fitowa.
"Ya daga waya ya kira dayan wanda ake zargin wanda ya isa wurin da wata motar, sai dai ta lalace a take.
"Wadanda ake zargin sun nemi taimako daga wata kungiyar 'yan sa kai dake Jaji-Maji. Lokacin da kungiyar ta iso wurin, sai aka samu gawar Aisami," kakakin 'yan sandan yace.
Abdulkarim ya kara da cewa, kungiyar 'yan sa kan ta gaggauta kiran 'yan sanda inda aka cafke wadanda ake zargin.
Ya bayyana cewa, 'yan sandan sun samo bindiga da motocin biyu inda ya kara da cewa ana kokarin gano su waye wadanda ake zargin.
Abdulkarim yace za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike a kansu.
A daya bangaren, gwamna Mai Mala Buni na jihar ya bayyana damuwarsa kan kisan gillar da aka yi wa Shehin Malamin.
A takardar da Buni ya saki a Damaturu ta hannun darakta janar na yada labarai, Alhaji Mamman Mohammed, ya kwatanta lamarin da ke tattare da kisan da abun takaici, nadama kuma mara dadi.
Gwamnan ya jajanta wa iyalan mamacin, jama'ar karamar hukumar Bade da dukkan mutanen jihar kan mutuwar Aisami.
Buni yayi kira garesu da su kwantar da hankalinsu kuma su kasance masu bin doka yayin da ake cigaba da bincike.
Asali: Legit.ng