Zamu Dira Kan Barayin Man Fetur A Neja-Delta, Shugaba Buhari
- Biyo bayan damke jirgin mai yana satar danyen man Najeriya a Neja Delta, Shugaba Buhari ya fusata
- Kulli yaumin ana wawurar dukiyar Najeriya sakamakon fasa bututun mai ana kwashe danyan mai
- Shugaban kasan ya ce jami'an tsaro su gaggauta damke masu kokarin talauta Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a karfafa tsaro domin dakile masu satar danyan man Najeriya.
Buhari ya bayyana hakan ne mako guda bayan da aka damke jirgin ruwa yana kokarin satar man Najeriya, rahoton ChannelsTV.
Shugaban kasar yace:
"Ba zamu bari wasu yan tsiraru su rika sace dukiyar danyan man kasa ba, saboda haka na umurci jami'an tsaro su gaggauta dakatar da aikin masu fasa kwabri a Neja Delta."
"Kada a bari su tsira, kuma muna karfafa hadin kai da kasashen da makwabta don kawo karshen yan ta'addan."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami'an Sojin Ruwan Najeriya Sun Damke Jirgin kasar Norway Yana Satar Danyen Man Najeriya
A ranar 12 ga Agusta, Jami'an Sojin ruwan Najeriya sun damke wani jirgin ruwa, (MT) HEROIC IDUN, mallakin kamfanin Hunter Tankers AS dake Scandinavia, Norway yana kokarin satar danyan mai a Najeriya.
Jami'in tsare-tsare da shirye-shiryen hukumar, Saidu Garba, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma'a.
Hukumar ta bayyana cewa jirgin ruwan ya isa rijiyar man ne cikin daren 7 ga Agusta da niyyar satar mai amma jami'anta suka dakilesu.
Saidu Garba ya cigaba da cewa sakamakon haka suka umurci direban jirgin ya jira sai NNPC ya bashi izini, amma Direban ya kurewa jirginsa gudu kuma ya nufi kasar Sao Tome and Principe, riwayar TheCable.
A cewarsa, daga baya aka damke jirgin ruwan a kasar Equatorial Guinea bayan kure masa gudu.
Babban Lauyan kasar Equitorial Guinea, Anatalio Nzang Nguema, ya bayyanawa tashar Talabijin na TVGE cewa an damke mutum 25 ke cikin jirgin.
Sun hada da yan kasar Indiya 16, yan kasar Sri Lanka 7, dan kasar Poland daya da kuma dan kasar Filibbin daya.
Kulli yaumin ana wawurar dukiyar Najeriya sakamakon fasa bututun mai ana kwashe danyan ma.
Asali: Legit.ng