Aikin Gwamnati Fa Ba Wajen Zuba Jahilai Marasa Aikin Yi Bane, Shugaba Buhari

Aikin Gwamnati Fa Ba Wajen Zuba Jahilai Marasa Aikin Yi Bane, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yace aikin gwamnati na mutane mafi kwazo da kokari cikin al'umma ne
  • Buhari ya yi gargadin cewa aikin gwamnati ba wajen jibge marasa aiki masu neman aiki kawai bane
  • Gwamnatin tarayya na daukan ma'aikata a fannoni daban-daban don yiwa kasa aiki

Abuja - A ranar Juma'a, 19 ga watan Augusta, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa aikin gwamnati fa ba wajen ajiye jahilai marasa aikin yi bane masu neman aiki.

ChannelsTv ta ruwaito shugaban kasan ya bayyana hakan yayin karban bakuncin Shugabar ma'aikatan gwamnatin Najeriya, Folashade Yemi-Esan da Shugaban kungiyar manyan ma'aikatan gwamnatin Najeriya, Innocent Boka-Audu a fadar shugaban kasa.

Buhari ya cewa kamata yayi aikin gwamnati ya matattarar mutane mafi kwazo da kwakwalwa cikin al'umma don magance matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

Goro a miya: Gwamnoni sun taru a Aso Rock don tattauna batun tattalin arziki, Buhari bai halarta ba

Shugaban kasa ya bayyana cewa lallai akwai bukatar karawa ma'aikata albashi musamman sakamakon hauhawar tattalin arziki.

Yace amma a sani abubuwa sun yiwa gwamnati yawa musamman rashin kudi da masu satar danyan man Najeriya.

Buhari
Aikin Gwamnati Fa Ba Wajen Zuba Jahilai Marasa Aikin Yi Bane, Shugaba Buhari Hoto: Presindency
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an Sojin Ruwan Najeriya Sun Damke Jirgin kasar Norway Yana Satar Danyen Man Najeriya

Game da satar danyan mai, jami'an Sojin ruwan Najeriya sun damke wani jirgin ruwa, (MT) HEROIC IDUN, mallakin kamfanin Hunter Tankers AS dake Scandinavia, Norway yana kokarin satar danyan mai a Najeriya.

Jami'in tsare-tsare da shirye-shiryen hukumar, Saidu Garba, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma'a, rahoton Premium Times.

A cewarsa, jirgin ya shigo Najeriya ne kuma kai tsaye ya nufi rijiyar man Akpo ba tare da izinin kamfanin NNPC ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel