Da duminsa: Yan bindiga Sun Sako Kwamishanan Jihar Nasarawa
- Bayan kwanaki hudu a kurmin daji tsare hannun yan bindiga, babban jami'in gwamnati ya kubuta
- Rikicin yan bindiga ya fara shiga jihar Nasarawa, Arewa maso tsakiya Najeriya kwanakin nan
- Jami'an tsaro na ikirarin samun nasarori wajen halaka yan bindigan a yankin Arewa maso yamma
Nasarawa - Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako Kwamishanan labaran jihar Nasarawa, Hanarabul Mohammed Lawal Yakub, bayan kwashe kwanaki hudu hannunsu.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana hakan ne a hirar wayar tarho, rahoton Leadership.
Ya bayyana cewa Kwamishanan ya samu yancin ne ranar Juma'a, 19 ga Agusta, 2022.
Ya kara da cewa tuni an garzaya da kwamishanan asibiti domin duba lafiyarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun Nemi Kudin Fansa N100m
A baya yan bindigan sun bukaci a biya su N100m a matsayin kudin fansa.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa an sace Yakubu ne a gidansa da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon da yammacin ranar Litinin 15 ga watan Agusta.
Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tona cewa masu garkuwa da mutanen sun bayyana bukatarsu ne a ranar Talata.
Ya ce tsagerun sun kira da misalin karfe 4:30 na yamma ta wayar daya daga cikin iyalan kwamishinan, sun sha alwashin ba za su karbi kasa da N100m kafin su sako shi.
Asali: Legit.ng