Farashin Iskar Gas na Girki Yayi tashin Ninki cikin Shekara 1, Cibiyar Kididdiga NBS

Farashin Iskar Gas na Girki Yayi tashin Ninki cikin Shekara 1, Cibiyar Kididdiga NBS

  • Rahoton bincike ya nuna yadda farashin iskar Gas yayi tashin gwauron zabo cikin shekara guda kacal
  • Yanzu duk magidancin da ya tanadi kudin Gas a bara, yana biyan ninkin kudin don sayan Gas na girki
  • Jihar Ebonyi ce tafi tsadar iskar Gas a watan Yuliinda har dubu goma sha daya an siyasa tukunyar 12.5kg

Abuja - Cibiyar Kididdiga da Lissafi ta Najeriya ta bayyana cewa farashin cika tukunyar 12.5kg na iskar gas din girki ya karu da alkaluma 122.15% cikin shekara guda.

Hakan na nufin cewa yanzu yan Najeriya na siyan iskar gas 12.5KG a kudi N9,824.07 sabanin N4,422.32 da suka saya a watar Yuli, 2021.

NBS ta bayyana hakan ne a sabon rahoton da ta fitar game da farashin iskar Gas a watan Yuli a shafinta na Tuwita.

Kara karanta wannan

Jihohin Najeriya 10 Da Matansu Ke Kan Gaba Wurin Kwankwaɗar Barasa, Kamfanonin Giya Sun Samu N542bn Cikin Wata 6

Rahoton yace:

"Farashin cika tukunyar Gas 125kg ya tashi da alkaluma 3.56% cikin wata guda tsakanin Yuni da Yuli, 2022. Yayinda aka saya N9,485.91 a June 2022 , ya koma N9,824.07 a Yuli 2022."
"Tsakanin Yulin 2021 da Yulin 2022 kuwa, ya tashi ninki 122.15%."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A lissafin dalla-dalla, jihar Ebonyi farashin yafi tashi inda aka sayar N11,212 sannan jihar Delta da aka sayar N10,926, sai Ekiti N10,883.67."

Shin Najeriya ci baya ake ko gaba? Ga Farashin Abubuwa goma (10) a 2015 da yanzu

An rantsar da shugaba Muhammadu Buhari ranar 29 ga watan Mayu 2015 tare da mataimakansa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Shekaru bakwai yanzu, yan Najeriya na tambaya, shin Najeriya ta cigaba ne daga 2015 zuwa yanzu ko kuma ci baya ake samu?

Jaridar Business Day ta jeranto farashin wasu abubuwa masu muhimmanci a rayuwar yau da kullum yadda suke a 2015 da yadda suke a yau.

Kara karanta wannan

Ana Za a Bar Mulki, Tsohon ‘Dan Majalisa yace Ganduje Bai Ci Zaben 2019 ba

Ga jadawalin:

Farashin Filawa

2015: N7,000

2022: N26,500

Farashin Burodi

2015:N300

2022 :N700

Farashin buhun Shinkafa

2015: N8,700

2022:N32,000

Farashin Taliya

2015: N180

2022: N400

Farashin Kifi (1kg)

2015: N900

2022: N2,200

FFarashin Manja (25 lita)

2015: N6,500

2022: N20,000

Farashin Kwai kiret

2015: N700

2022: N2000

Farashin Litan Man Diesel

2015: N145

2022: N8000

Farashin Gas na girki (12.5Kg)

2015: N3,200

2022: N10,000

Farashin Tikitin Jirgi

2015: N15,000

2022: N50,000

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida