Kakar Abba Gida-Gida, Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar NNPP A Kano Ta Rasu

Kakar Abba Gida-Gida, Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar NNPP A Kano Ta Rasu

  • Kakar dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta rasu
  • Za a yi jana'izar Hajiya Mowa Sufi Yakasai a fadar mai martaba sarkin Kano bayan sallar Juma'a
  • Marigayiyar ta rasu bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya, tana da shekaru 103 a duniya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Allah ya yiwa Hajiya Mowa Sufi Yakasai, kakar dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, rasuwa.

Hajiya Yakasai, wacce ke da shekaru 103 a duniya ta rasu bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Abba Kabir da kakarsa
Kakar Abba Gida-Gida, Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar NNPP A Kano Ta Rasu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Za a yi jana’izarta a fadar mai martaba sarkin Kano bayan sallar Juma’a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Daga cikin ‘ya’yanta akwai tsohon sakataren ilimi na kwalejin karatun Musulunci da shari’a na Aminu Kano (AKCILS), Ibrahim Abubakar Aminu.

Kara karanta wannan

Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta rasu ta bar yara da jikoki da yawa wadanda a cikinsu harda wani likita a babban asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Dr Atiku Musa.

Dattijuwa Mai Shekaru 60 Ta Haifi Yan Uku Bayan Shafe Tsawon Lokaci Tana jiran Tsammani, Hotuna

A wani labari na daban, bayan tsawon shekaru da dama tana jiran tsammani, Allah ya albarkaci wata yar Najeriya mai suna Chinwe Mbahotu da haihuwar yan uku.

Mbahotu, wacce shekarunta suka haura 60 a duniya ta haifi maza biyu da mace daya.

Wani dan uwan matar, Cliff Ayozie, ne ya wallafa labarin mai dadi a shafin Facebook, inda ya bayyana cewa ta haihu ne a Dallas, kasar Amurka a cikin makon jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng