Wani Mutumi Ya Zargi Iyayen Matarsa da Yin Garkuwa da Sahibarsa

Wani Mutumi Ya Zargi Iyayen Matarsa da Yin Garkuwa da Sahibarsa

  • Abu kamar wasan kwaikwayo, wani mutumi ya kai ƙarar Surukansa kan zargin sun yi garkuwa da matarsa woto diyarsu a Suleja, jihar Neja
  • Mai shigar da ƙara a Kotu daga hukumar yan sanda ya gaya wa Alƙali cewa mutanen biyu sun je har gidan diyarsu sun tafi da ita
  • Wannan na zuwa ne a lokacin mutane suka tsinci gawar mutum biyu mace da namiji a Kango duk a yankin na Suleja

Niger - An gurfanar da iyayen wata matar aure da ke zaune a Kwankwashe, yankin ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja a gaban Kotun Majistire da ke zamanta a Madalla.

Jaridar Daily Trust ta ruwiato cewa hukumar yan sanda ta gurfanar da iyayen matan a Kotu ne bisa zargin sun sace ɗiyar su daga gidan Aurenta.

Wani ya kai surukansa ƙara Kotu.
Wani Mutumi Ya Zargi Iyayen Matarsa da Yin Garkuwa da Sahibarsa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mai shigar da ƙara, ASP John Ateni, ya faɗa wa Kotun cewa mutumin da ake zargi, Godgift Ekwedi, da matarsa, Eshima Ekwedi, sun dira gidan ɗiyar su da ke yankin Rafin Sanyi a Suleja, suka yi awon gaba da ita ba tare da izinin mijinta ba.

Kara karanta wannan

Yadda Ma'aikata Masu Ɗaukar Albashi a Najeriya Suka Koma Tafiyar Kafa Saboda Tsadar Kuɗin Mota

Bugu da ƙari a cewar mai shigar da karar, sun kwashe kayayyaki a gidan auren ɗiyar ta su wanda a kiyasi sun kai darajar Miliyan biyu da rabi, daga bisani suka cigaba da amfani da kayan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Waɗan da ake zargin sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka ɗora kansu kuma suka nemi Kotu ta ba da belin su.

Alƙalin Kotun, Mai shari'a Ruth Ibrahim, ta bai wa waɗan da ake ƙara beli bisa sharaɗin kawo wanda zai tsaya musu kuma tilas ya zama mazaunin Madalla.

Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Alkalin Kotun ta sanar da ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 5 ga watan Satumba, 2022.

A wani labarin kuma An tsinci wawar wani Mutumi da wata mace a wani Kango tsirara a yankin Suleja

Mutane sun tsinci gawarwakin wasu mutum biyu, namiji da mace tsirara a wani Kango a yankin karamar hukumar Suleja, jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Gida-Gida, Sun Kashe Mutane Sun Sace Wasu Da Dama

Mutumin da ya fara ganin gawarwakin ya bayyana yadda ya gan su yayin da yaje kusa da Kangon yin bayan gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: