Matsin Rayuwa Ta Sa Masu Daukar Albashi Fara Tafiyar Kafa Maimakon Hawa Bas
- Farashin kudin tafiye-tafiya a motar haya na ƙara tashi biyo bayan ƙarin farashin Litar Fetur a Najeriya
- Wasu masu ɗibar Albashi sun fara maye gurbin shiga motar Bas zuwa wurin aiki da tafiyar kafa domin rage kuɗi
- A jihar Legas, lamarin ya tashi daga sabon abu ya koma salon tafiyar da rayuwa da mutane suka saba da shi na yau da kullum
Farashin hawa motocin haya Bas na ƙara tashi a kowace rana kuma hakan ya bar ma'aikata masu ɗaukar Albashi da neman wani zaɓin, kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro.
A halin yanzu kuɗin tafiyar Kilo Mita 10 ya tashi da kusan kaso 100 kuma hakan babban lamari ne da ya zarce wasa a wurin mai ɗaukar Albashi, wanda sai an kai ruwa rana sannan ake karɓar bukatarsa ta karin Albashi.
Don haka, idan kaga tawagar mutane na taka sayyadar kafar su karka ɗaga hankalinka, mutane na duba hanya mafi sauki da zasu rayu.
Duk da lamarin abun damuwa ne da takaici, amma abu ne mai matuƙar muhimmanci ka rayu a ƙasar da masu kasuwancin mai suka maida farashin litar Fetur a tsakankanin N175 da N230.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tattalin Arziki da Salon tafiyar da rayuwa sun nuna cewa farashin tafiye-tafiye ya tashi da kaso sama da 90% a 'yan watannin da suka shuɗe bayan yan kasuwa sun ƙara farashin Fetur.
Yadda Mutane suka rungumi tattaki
Wani ma'aikacin wucin gadi a jihar Legas, wanda ke aiki a fannin gine-gine, Saheed Abodunrin, ya ce:
"Yanayin yadda abubuwa ke kara muni a ƙasar nan abun damuwa ne, albashi na bai karu ba tun 2020. Ga shi irin aikin mu babu lokacin da zaka taɓa wasu sana'o'i. Wata rana a tasha na gano kuɗin mota ya karu da kashi 100."
"Lokacin da na isa gida na kashe N3,500 daga Agbaraa zuwa Island zuwa gida. Ban taɓa ware wa tafiyar abinda ya wuce N2,000. Washe gari sai na yanke tafiya a ƙafa mai nisa zuwa tasha, bayan na sauka a CMS na sake tafiya a ƙafa zuwa Ofis."
"Yanzun kafin na bar gida na kan duba taswira don ganin hanyar dake da cunkoso na kauce mata na rage kashe kuɗi. Gaskiya yanzun na kan rage N800, haka wasu abokan aiki na suke yi don kuɗin da suke ware wa su ishe su a wata."
Adebisi Okunowo, wani Sakatare da ke aiki a Mainland ya ce:
"Tun watan Yulin wannan shekarar, ina jira na tsawon lokaci don samun Direba mai kirki da zai faɗi kuɗin da ya dace. Yanzun kuɗin Bas daga Mile 2 zuwa Iyana-Iba wanda N100 ne yanzu ya koma N400. Ina jiran Motar N200 kullum."
Duk da tafiya a ƙafa na ɗaya daga cikin motsa jikin da ke ƙara lafiya, amma idan ya yi yawa kuma yana da illa a jikin mutum.
Wani Akanta kuma Tela a jihar Legas, Usen Abednego, ya ce:
"Tafiya a ƙafa yanzun a Legas saboda tashin kuɗin Bas ba wani sabon abu bane domin ya koma cikin yanayin rayuwa. Ina takaicin ganin mutane na taka wa a ƙafa ba don motsa jiki ba saboda ba zasu iya biyan kudin mota ba."
"Matsalar shi ne wannan dogon tafiyan a ƙafa wanda yanzu kusan ya zama jiki yana haddasa haɗari da mutane ko a tare su a musu fashi, a wani hangen kuma yana jawo gajiya da zata hana aiki yadda yakamata."
A wani labarin kuma NAHCON ta kammala kwaso Alhazan Najeriya daga kasa mai Tsarki, ta yi magana kan matsalolin da aka samu
Hukumar jin daɗin Alhazai ta ƙasa NAHCON ta kammala dukkan ayyukan aikin Hajjin 2022 bayan jirgin karshe ya baro Jiddah.
Shugaban Hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya amince da matsalolin da aka samu da kuma matakin da zasu ɗauka a gaba.
Asali: Legit.ng