NDLEA Ta Kama Tsohon Soja Dan Shekara 90 Dake Kai Wa Yan Bindiga Kwayoyi
- Hukumar NDLEA ta kama wani tsohon Soja ɗan shekara 90 a duniya da ke aikin kaiwa yan bindiya kwayoyi a Sakkwato
- Mai magana da yawun hukumar ya ce mutumin ya shiga hannu ne a kauyen Mailalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni
- Haka zalika Bsbafemi ya bayyana wasu nasarori da jami'ai suka samu a wasu sassan Najeriya
Sokoto - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce dakarunta sun kama wani Soja mai ritaya ɗan shekara 90 bisa zargin kai wa yan bindiga miyagun kwayoyi.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya ce mutumin mai suna Usman Adamu, ya shiga hannu ne a Mailalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni, jihar Sakkwato.
The Cable ta rahoto kakakin hukumar na cewa an kama wanda ake zargin ɗauke da hodar Iblis mai nauyin Kilo 5.1kg.
Dakarun NDLEA sun samu wasu nasarori
Babafemi ya ƙara da cewa a wata nasarar ta daban, dakarun sun yi ram da wani, Anietie Okon Effiong, wanda aka gano Malamin Coci ne kan zargin hannu a shigo da wata kwaya daga ƙasar Indiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Abun mai nauyin kilo 90kg kuma aka ɗoro shi a wata Motar Bas mai lamba RSH 691XC a Ojuelegba, jihar Legas sun shiga hannu a wurin shingen bincike kan hanyar Umuahia-Ikot Ekpene ranar Asabar 6 ga Agusta."
"Kwayar mai hatsari an zuba ta a Durom mai cin kilo 30kg guda biyu mallakin Faston, wanda kuma an kama shi yayin da aka bi diddigin shi a Aron."
Ya ƙara da cewa wani ɗan asalin ƙaramar hukumar Ovia, jihar Edo dan kimanin shekara 37 a duniya mazaunin Italy, Solo Osamede, ya shiga hannun jami'ai ranar 30 ga watan Yuli.
An kama mutumin ne a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas kan haɗiye ƙunshin tabar Heroic guda 41.
Ya shiga hannu ne yayin da yake kokarin hawa jirgin saman Turkish Airline zuwa birnin Milan na ƙasar Italiya, Leadership ta rahoto.
A wani labarin kuma Gwamnonin Sun Lissafo Hanyoyi Shida da CBN Ya Bi Wajen Lalata Darajar Naira
Gwamnonin Najeriya sun lissafa abubuwa Shida da suka ganin sun jawo faɗuwar darajar Naira a kasuwar duniya.
Haka nan gwamnonin sun ba shugaban ƙasa shawarwarin da za'a bi don ceto Najeriya daga durkushewar tattalin arziki.
Asali: Legit.ng