Bidiyo: Budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta fallasa yadda matar mamacin ke yi masa barbaɗe a abinci

Bidiyo: Budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta fallasa yadda matar mamacin ke yi masa barbaɗe a abinci

  • An shiga tashin hankali da hargitsi a wurin wata jana'iza bayan wata budurwa ta hau kan mumbari tare da bayyana kalaman karshe na mamacin
  • Kamar yadda budurwar ta bayyana, ta kwashe kwanaki uku tare da mamacin kuma ta tambaye shi abinda ya kashe shi har lahira
  • Ta zargi cewa, mamacin mai suna Paul ya zargi matarsa ta aure da yi masa barbaden wasu abubuwa a cikin abincinsa

Wata budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta bayyana kalaman karshe na mamacin wanda tace da kanshi ya bayyana mata.

A wani bidiyo da @natnats41 ta saka a TikTok, budurwar ta haye mumbari kuma tayi jawabi ga masu makokin mutuwar.

Tarzoma
Bidiyo: Budurwa ta hargitsa wurin jana'iza bayan ta fallasa yadda matar mamacin ke yi masa barbaɗe a abinci. Hoto daga TikTok/@natnats41
Asali: UGC

Ta fara ne ta hanyar jero sunayen 'ya'yan mamacin sannan ta fallasa wacce take zargin ta halaka shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa

Budurwar da tayi ikirarin cewa ta kwashe kwanaki uku da mamacin inda ta tambaye shi abinda ya kai shi kwance kuma kai tsaye ya bayyana abinda ke niyyar aika shi barzahu.

Ta kara da bayyana cewa, mamacin mai suna Paul ya sanar da ita cewa matarsa ce take yi masa barbaden wasu abubuwa a cikin abinci.

Wannan jawabin na budurwa kuwa ya hargitsa wurin gaba daya.

Kalla bidiyon:

Jama'a sun yi martani

Elias Jib Samuel yace: "Faston ya hadu da yake kokarin kwantarwa da jama'a hankali, yace " wannan farmaki ne na kai tsaye daga makiya."
Just Jorden yace: "Faston ya cancanci kambun yabo ganin yadda ya kwantar da wannan tarzomar."
Desperado yace: "Daga farko, ya yi kama da dirama amma tsokacin da aka dinga yi ne ya ja hankalina."
Missyfoodworld3 tace: "Ba zan yi karya ba, da a ce ina wurin kuma na ji wannan zancen, babu shakka dariya zan kece da ita in manta cewa mun je makoki ne."

Kara karanta wannan

Bidiyon doguwar budurwa mai shekaru 22, tana da tsayin ban mamaki

Ras kwana uwar lissafi: Bankin duniya ya dauka nauyin karatun hazikar Bakanuwar yarinya

A wani labri na daban, an sake daukar nauyin karatun Saratu Dan-Azumi, karamar yarinya daga jihar Kano wacce ta kware a lissafi.

A cikin kwanakin nan ne aka gano cewa yarinyar da ta bar makaranta amma take iya sarrafa lambobi kamar kwamfuyuta.

Gidauniyar Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa ne ya fara daukar nauyin yarinyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng