ASUU: Lakcarorin Jami'ar Kaduna Sun Bijirewa Umurnin El-Rufai, Sun Ki Zuwa Yi Wa Dalibai Jarrabawa

ASUU: Lakcarorin Jami'ar Kaduna Sun Bijirewa Umurnin El-Rufai, Sun Ki Zuwa Yi Wa Dalibai Jarrabawa

  • Malamai a Jami'ar Jihar Kaduna wato KASU, mambobi na kungiyar ASUU sun ki komawa bakin aiki duk da barazanar kora da Gwamna El-Rufai ya yi
  • Malaman, cikin wani sanarwar bayan taro mai dauke da sa hannun shugaban ASUU da sakatare na jami'ar sun ce ba su yi wa daliban jarrabawa ba don har yanzu ba dage yajin aiki ba
  • Sun ce akwai matsaloli tattare da jarrabawar, kuma za su tattara bayanai su tura wa hukumar kula da jami'o'i kana za su hukunta malaman da suka yi wa dalibai jarrabawar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya, ASUU, reshen Jami'ar Kaduna (KASU) ta ki komawa aji duk da barazanar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi na cewa zai kore su.

Mahukunta a makaranatar sun bukaci dalibai su dawo aji domin su cigaba da jarrabawansu bayan barazanar da gwamnan ya yi.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Jami'ar Kaduna ta yi watsi da rikicin ASUU da Buhari, ta ci gaba da karatu

Jami'ar Kaduna.
ASUU: Lakcarorin Jami'ar Kaduna Sun Saba Umurnin El-Rufai, Sun Ki Zuwa Yi Wa Dalibai Jarrabawa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A ranar Litinin, an ga wasu daliban a aji suna rubuta jarrabawa inda shugaban jami'ar da wasu malamai ke duba su.

Daily Trust ta gano cewa mambobin ASUU ba su shiga cikin wadanda ke duba daliban da ke rubuta jarrabawar ba suna ikirarin cewa har yanzu suna yajin aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar, a karshen wani taro da ta yi a Jami'ar ta Kaduna a ranar Litinin ta ce akwai matsaloli tare da jarrabawar.

Shugaban ASUU na jami'ar ta KASU, Kwamared Peter Adamu, da sakatarenta Kwamared Usman Abbas ne suka saka hannu a sanarwar.

Sanarwar ta ce:

"Kungiyar za ta tattara dukkan matsalolin da ta lura da shi a yayin jarrabawar da aka yi ta tura wa hukumar kula da jami'o'i na kasa.
"Mambobin ASUU na KASU ba su yi wani jarrabawa ba domin yajin aikin da ake yi har yanzu kuma ba za su gajiya ba.

Kara karanta wannan

Bayan Barazanar Gwamna El-Rufai, Malaman Jami’a Sun Koma Aiki a Kaduna

"Ana lura da dukkan saba dokoki da mambobin suka yi kuma za a hukunta su bisa dokokin kungiyar a lokacin da ya dace," in ji shi.

Martanin Shugaban KASU

A bangarensa, Shugaban Jami'ar ta KASU Farfesa Abdullahi Ashafa, ya ce a makarantarsu, KASU-ASUU ta shiga yajin aikin ne don kara ga jami'o'in tarayya amma matsalolin da ake yajin aikin saboda su ba su shafe su ba.

"Don haka ya kamata mu zama masu kishin kasa, daliban mu sun zauna gida fiye da watanni biyar kuma babu alamar za a warware matsalar.
"Jiya, an kara tsawaita yajin aikin da makonni hudu, amma abin da ASUU ke nema wurin gwamnatin tarayya bai shafe mu ba," in ji shi.

Yajin Aikin ASUU: Wasu Dalibai Sun Zama Masu Garkuwa Da Mutane, In Ji Shugaban Kungiyar Kwadago, NLC

A wani rahoto, hukumar Kwadago ta Najeriya, NLC, reshen Jihar Enugu, a ranar Talata ta shiga yajin aikin goyon bayan ASUU da ake yi a kasar.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun shiga tasku: ASUU ta tsawaita yajin aikinta zuwa karin wasu makwanni masu yawa

ASUU da sauran kungiyoyi a bangaren ilimi sun shiga yajin aiki kan rashin amincewa da yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnati.

Duk da cewa yajin aikin an fara shi ne na gargadi na mako hudu, ASUU ta cigaba da tsawaita yajin aikin duk lokacin da wa'adin gargadin ya kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164