Girmamawa: Obasanjo ya gana da sabon basarake, ya durkusa masa don gaida shi
- A ranar Litinin, 1 ga watan Augusta, 'yan asalin Owu da masu nadin sarauta a jihar Ogun sun karba sabon Olowu na Owu, Saka Matemilola
- Sabon basaraken farfesa ne wanda ya samu darewa kujerar sarautar sakamakon gadon da yayi kaka sa kakanni
- Abun sha'awa shine yadda tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya karba basaraken kuma ya durkusa wurin gaishesa
Ogun - A ranar Litinin, 1 ga watan Augustan 2022, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya karba bakuncin Saka Matemilola Adelola, sabon Olowu na Owu, a gidansa dake Abeokuta na jihar Ogun.
Obasanjo, wanda shi ke da sarautar Balogun din Owu, ya karba sabon basaraken tare da 'yan Owu da kuma masu nadin sarauta a gidansa na Ita-Eko dake karamar hukumar Abeokuta ta arewa.
Kamar yadda TheCable ta rahoto, tsohon shugaban kasan ya durkusa a gaban Olowu domin yi mishi maraba da zuwa.
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kayayyaki Ke Cigaba Tashi A Kasar
Daga gidan Obasanjo, an jagoranci sabon basaraken zuwa fadar Adedotun Gbadebo, Alake na Egbaland, domin mika gaisuwa inda daga nan aka kai shi Oke-Ago Owu domin fara shirin nadin sarautar, Premium Times ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Obasanjo ya yabi matasa da gwamnatin jihar
Obasanjo ya mika godiya ga duk wanda ke da hannu wurin zaben. Ya godewa gwamnatin jihar da ta amince da Metemilola a matsayin sabon Olowu kuma ya tabbatar da cewa sabon basaraken zai samu goyon bayan jama'a tare da mulki cikin kwanciyar hankali.
Matsin Rayuwa: Farashin Litar Kalanzir ya kai N800, Ƴan Najeriya sun Shiga Halin Ha'u'la'i
A wani labari na daban, farashin kalanzir wanda iyalai da yawa ke amfani da shi, yayi tashin gwauron zabi zuwa N800 matsayin kudin lita daya saboda yadda kasuwar ke kokarin juyawa tare da daidaitawa zuwa sabon karin farashin man fetur da iskar gas.
Binciken kasuwa da The Punch tayi a ranar Talata ya bayyana cewa, a makon da ya gabata an siyar da kalanzir kan farashin N700 lita daya amma yanzu ana siyar da shi kan N800 zuwa N850 a wasu sassan birnin Legas, yayin da farashin ya kai N1000 a wasu wuraren.
A Ghana, farashin litar kalanzir a halin yanzu ya kai N585 wanda daidai yake da GH 12.044.
Asali: Legit.ng