Mutane Sun Kusa Fara Kalaci Da Junansu, Dan Najeriya Ya Koka Da Tsadar Biredi A Kasar, Bidiyo

Mutane Sun Kusa Fara Kalaci Da Junansu, Dan Najeriya Ya Koka Da Tsadar Biredi A Kasar, Bidiyo

  • Jama'ar Najeriya sun fara gajiya da yadda farashin abubuwa musamman abinci ke kara hauhawa a kullun
  • Bidiyon wani dan Najeriya ya yadu inda ya koka kan yadda farashin biredi ya yi tashin gwauron zabi
  • Ta kai har mutumin ya furta cewa yadda abubuwa suke a yanzu, mutane sun kusa fara cinye junansu

Wani mutumin Najeriya ya je shafin soshiyal midiya don kokawa a kan yadda farashin biredi ke tashin gwauron zabi a kasar.

A wani bidiyo da mutumin ya yi a cikin wani shagon siyar da biredi wanda shafin LIB ya wallafa, an gano yana korafi cewa sinkin biredi da ake siyarwa kan N300 ya zama N800 a yanzu.

Biredi
Mutane Sun Kusa Fara Kalaci Da Junansu, Dan Najeriya Ya Koka Da Tsadar Biredi A Kasar, Bidiyo Hoto: lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Ya kuma bayyana cewa yadda abubuwa suka koma a yanzu, yan Najeriya sun kusa fara yin kalaci da junansu.

Kara karanta wannan

An Sha Fama: Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na siya wannan biredin a watan da ya gabata N550, sai suka fara siyar da shi N600 yan makonni da suka gabata, yanzu kuma N800 ne. N800 fa kudin biredin da ake siyarwa N250 ko N300. Ni kadai ina iya cinye wannan biredin ina ga mutum mai yara hudu.
“A haka ne wani zai je gefe yana goyon bayan shirme, ku kalla yadda abubuwa ke tafiya a yanzu, lokaci zai zo da yan Najeriya za su fara kalaci da junansu.”

Jama'a sun yi martani

luxury_hairsbyneche ta yi martani:

"Biredin da muke siyasa #480 na siye shi kan 1100 da yamman nan."

chioma_gold15 ta ce:

"Biredi yanzu na masu kudi ne, na siya yau #800"

nana.thriftcloset ta ce:

Na gama da biredin #500 yau Allah mun tuba"

Legit.ng ta tuntubi wasu mutane don jin yadda abun yake a wajensu.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ana Tsaka Da Ruwan Sama, Tsoho Ya Rikewa Matarsa Lema Cike Da Kauna

Wani ma'aikacin gwamnati mai suna Mallam Abubakar ya ce abun babu sauki domin shi kansa biredin da yake siya #500 ya koma #700.

Ya ce:

"Abun dai ba a cewa komai amma talaka na ganin jarabawa, a nan Landmark biredin #500 ya koma #700 kuma kada kace ko an kara girmansa ne, a'a yana nan yadda yake."

A nashi bangaren, wani magidanci mai suna mallam Ibrahim Ndanusa ya ce shi ya kusa daina cin biredi a gidansa yadda abubuwa ke tafiya yanzu.

"Ai biredi na mai kudi ne, na fadawa matata zan dunga siyo dan filawa tana murzawa idan har dole sai an ci din, amma abun ba sauki."

Rarara Ya Shirya Taron Saukar Al-qurani Don Samun Zaman Lafiya A Kasar, Jarumai Maza Da Mata Sun Hallara

A wani labarin, shahararren mawakin nan na siyasa kuma shugaban mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gudanar da wani taron addu’a na musamman.

Kara karanta wannan

Yadda Wata Amarya Da Kawayenta Suka Yi Shiga Ta Kamala, Bidiyon Ya Burge Mutane

Rarara wanda ya kuma kasance jagoran tafiyar 13X13 na masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, ya tara malamai inda aka yi saukar Al-Kur’ani domin ci gaban kasar.

Kamar yadda jarumi kuma MC Mallam Ibrahim Sharukan ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce an yanka rakuma biyu bayan addu’an domin tabbatar da zaman lafiyan kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng