Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Kashe Babban Basarake A Jihar Taraba
- Yan bindiga sun kashe Basaraken Masarautar Yakuben, ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba, Udeng Ibrahim Yamusa
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun kuma halaka direbansa wanda ya kasnace ɗansa kwanaki bayan sace su
- Taɓarɓarewar tsaro da ake fama da shi a sassan Najeriya ya sanya wasu Sanatoci sun fara tunanin tsige shugaban ƙasa
Taraba - Wasu mutane dauke da bindigu waɗan da ake zargin 'Yan bindiga ne sun halaka Ibrahim Yamusa, basaraken masarautar Yakuben, cikin karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.
Channels Tv ta samo cewa 'yan bindigan sun halaka matukin sa wanda kuma ya kasance dan sa ne.
Kafin halaka su, 'yan bindigan sun sace basaraken da dan na sa a ranar Alhamis, a wani kwanton bauna da su ka kai musu akan hanyar su ta dawowa daga Takum.
Sokoto: An Gano Gawarwakin Mutum 26 Da Suka Nutse A Ruwa Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, babban dan basaraken wanda kuma shine magatakardan sa, Fasto John Ibrahim, ya bayyana cewa an yi musu mummunan kisa akan hanyar su ta dawowa zuwa masarautar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yan bindiga sun shammaci mahaifina da danuwa na. Sun yanke shawarar tafiya a babur inda suka bar motar sa saboda rashin kyawun hanyoyin mu." A cewar sa.
Basaraken ya shirya halartar wani taron zaman lafiya a Takum, amma ya yanke shawarar dawowa gida saboda an dage taron.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka
Kakakin riko ta hukumar 'yan sandan jihar Taraba, DSP Kwache Gambo, ta tabbatar da aukuwar lamarin a daren ranar Asabar.
Ta bayyana cewa an gano gawarwakin basaraken da ta dan nasa a cikin wani daji can nesa da wurin da aka sace su.
A cewar Gambo, tuni aka fara bincike domin gano waɗanda ke da hannu akan kisan kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada umurni.
A wani labarin kuma yayin karɓan jiga-jigan APC da suka koma PDP, Atiku Abubakar ya ɗau alƙawarin kawo karshen yan bindiga
Atiku Abubakar ya kai ziyara jihar Zamfara, ya sha alwashin dawo da zaman lafiya idan ya ɗare kujerar shugaban ƙasa.
Ɗan takarar, wanda ya karɓi jiga-jigan APC da suka sauya sheka zuwa PDP, ya ce abu na farko da za'a fara yi shi ne kawar da APC daga mulki.
Asali: Legit.ng