Kin Gama Mun Komai a Rayuwa, Lauya Ya Fashe Da Kuka A Gaban Mahaifiyarsa Kan Dawainiyar Da Ta Yi Da Shi
- Wani lauya da aka rantsar a matsayin cikakken lauya ya burge mutane da dama a shafukan soshiyal midiya
- A wani bidiyo da ya yadu, an gano matashin kwance a gaban mahaifiyarsa, yana kuka da hawaye don nuna godiya kan dawainiyar da ta yi da shi
- Bidiyon ya taba zukata da dama a Instagram inda mutane da dama suka ce sun zubar da hawaye bayan kallon shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wani bidiyo mai taba zuciya da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno wani lauya da aka rantsar a matsayin cikakken lauya yana godiya ga mahaifiyarsa cike da kauna.
A cikin dan gajeren bidiyon, an gano matashin mai suna Harmonihie zube a gaban mahaifiyarsa yana zubar da hawayen murna da godiya.
Matashin ya rike kafafuwan mahaifiyar tasa yayin da yake kuka wiwi, yana godiya gare ta a kan goyon bayan da ta bashi a wannan tafiya na zama lauya.
Ya fadawa mahaifiyar tasa cewa ba don ita ba da bai zama komai ba a rayuwa, kuma bidiyon ya taba zukatan mutane da dama a soshiyal midiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dan gajeren rubutun da ya biyo bayan bidiyon ya sanyaya ran matar. Lauyan ya rubuta:
“Wacce ta mayar dani sarki, sarauniyata. Zan ci gaba da karrama ki mahaifiyata muddin rayuwa, duk yadda zan kai a rayuwa. Ke ce tushen rayuwata. Ban damu da kowaye ke kallo ba.”
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
@_aniscooser ta ce:
“Hakan ya yi kyau. Babu inda za ka je da addu’an iyayenka bai kai ba. Ina maka fatan alkhairi.”
@mizgrace5 ta yi martani:
“Allah ka albarkace ni na kula da mahaifiyata fiye da haka.”
@official_jimcally ya ce:
“Ya tabani. Uwa duniya ce.”
@domingo_loso ya yi martani:
“Haka take a nan, na san yadda kake ji. Ba don mahaifiyata ba da ban san ina zan kasance ba a rayuwa.”
Bayan Shekaru 15, Ma’aikacin Banki Ya Nemi Mai Gyaran Takalmin Da Ya Taimakesa, Ya Bashi Tukwici
A wani labari na daban, wani mutum ya ci ribar aikin al’khairin da ya taba yiwa wani matashi dan makaranta shekaru 15 da suka wuce a 2022.
Ma’aikacin banki dan kasar Ghana, Edward Asare ya bayyana yadda wani mai gyaran takalmi gurgu ya taimaka wajen gyara masa takalmin makarantarsa da ya baci a 2007.
A cewar Asare, yana a hanyarsa ta zuwa makaranta a wata rana kawai sai takalminsa ya lalace.
Asali: Legit.ng