Kano ta amince da karin kashi 50 na Kudin Tallafin Karatun Dalibai Marasa Galihu

Kano ta amince da karin kashi 50 na Kudin Tallafin Karatun Dalibai Marasa Galihu

  • Majalisar zartaswar ta jihar Kano ta amince da yiwa daliban jihar marasa galihu karin tallafin alawus zuwa kashi 50
  • Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya ce jimillar dalibai marasa galihu da za su ci gajiyar tallafin gwamnatin Kano sun kai 40,494 ne
  • Muhammad Garba ya ce za biya alawus din dalibai da ba a biya ba abaya a duka kananan hukumomin jiha

Jihar Kano - Majalisar zartaswar ta jihar Kano ta amince da karin kashi 50 cikin 100 na alawus din tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin jihar da ke halartar jami’o’in Najeriya. Rahoton TVC NEWS

Ta kuma ba da izinin sakin Naira miliyan 865.4 ga hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha a matsayin alawus da ba a biya ba da kuma samar da kayan aiki na biyan dalibai a fadin kananan hukumomin jihar 44 dake masarautu biyar.

Kara karanta wannan

Kano: Hotunan ragargazajjen asibiti inda mata ne tafiyar 3Km don zuwa haihuwa, ya tada hankalin jama'a

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron mako-mako da ya gudana a zauren majalisar.

KanoNI
Kano ta amince da karin kashi 50 na Kudin Tallafin Karatu Dalibai Marasa Galihu FOTO TVC NEWS
Asali: Twitter

Ya kara da cewa jimillar dalibai marasa galihu guda 40,494 ne za su ci gajiyar tallafin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, jimillar tallafin kudin karatu da aka baiwa kananan hukumomi 44 na jihar daga Karaye, Bichi, Rano, Gaya, da Kano ya kai Naira miliyan N836,269,150, yayin da kayan aikin biyan kudin ya kai N29,180,000.

Ya yi ikirarin cewa Masarautar Kano mai kananan hukumomi takwas, tana da guraben dalibai 26,086 da ba biya su ba, kuma za ta karbi Miliyan N538,974,000 baya ga Miliyan N13,100,000 na kayan aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa