Kyakkyawan Bidiyon ‘Yar Karamar Yarinya Tana Sarawa Sojoji Ya Kayatar Da Mutane
- Wata karamar yarinya kyakkyawa ta haddasa cece-kuce a shafin Twitter kan karamcin da ta nunawa wasu jami’ai da ke sanye da kayan sojoji
- Karamar yarinyar ta gano wasu sojoji sai ta je har inda suke sannan ta girmama su ta wani yanayi mai ban mamaki
- A wani bidiyo da ya yi fice, an gano yarinyar tana gudu zuwa wajen daya daga cikinsu sannan ta taba kafarsa kafin ta sara masu
Wani bidiyo na wata kyakkyawar yarinya karama tana karrama wasu jami’an sojoji ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan soshiyal midiya.
Karamar yarinyar ta gano jami’an tsaron sanye da kayan sojoji sai ta ruga da gudu zuwa wajensu. Sai ta taba kafar daya daga cikinsu sannan ta shafa goshinta da hannun nata.
Sojojin sun kalle ta cike da mamaki sannan duk suka yi mata murmushi cike da jin dadi. Sai ita murmusa kafin ta sara masu.
Masu amfani da shafin Twitter sun yi martani
Da suke martani ga bidiyon, mutane da dama sun nuna kaunarsu ga abun da yarinyar ta yi, wasu kuma sun ce ta nuna ita mai kishin kasa ce ta gaskiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dr Jess ya yi martani:
"Wadanda basu da ikon haduwa da jami’an sojoji suna iya taba kafafun masu gadinsu a kofar gida Jai Sri Ram."
Dominic Purs ya ce:
“Nuna girmamawa ga manyanku bai da alaka da daidaito. Yana nuna tawali’u kuma wannan al’ada ce ta musamman ga Indiyawa.”
Jayant Joshi ya ce:
“Karamar mutum mai kishin kasa. Na kalli wannan sau ba adadi kuma na kasa gajiya da shi.”
Bidiyoyin Wata Karamar Yarinya Tana Girgijewa Ya Burge Mutane
A wani labarin, jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wata kyakkyawar yarinya karama tana rawa.
A daya daga cikin bidiyoyin wanda shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram an gano yarinyar tana girgejewa tare da bin wata wakar turanci mai taken ‘Buga’.
Yanayin yarinyar da ke abubuwanta cike da wayo kamar ba yar shekarunta ba shi yafi daukar hankalin mutane.
Asali: Legit.ng