Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda A Jihar Kwara Ya Rasu A Hatsarin Mota

Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda A Jihar Kwara Ya Rasu A Hatsarin Mota

  • Ƙaramin mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar Kwara, ACP Abolade Oladigbolu, ya rasu sanadin haɗarin mota
  • Kakakin yan sandan jihar ya ce Marigayin ya hau ɗan Acaɓa ne sakamakon motarsa na gareji ta samu matsala
  • Kafin rasuwarsa, Marigayin ya kasance kwamandan yan sandan yankin Alapa, kuma ya jima yana hidimta wa kasa

Kwara - Mataimakin kwamishinan yan sanda a jihar Kwara, ACP Abolade Oladigbolu, ya rasa rayuwarsa a wani haɗarin mota da ya rutsa da shi.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kafin rasuwarsa ACP Oladigbolu, ya kasance kwamandan rundunar yan sanda na yankin Alapa, a jihar Kwara.

ACP Abolade Oladigbolu.
Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda A Jihar Kwara Ya Rasu A Hatsarin Mota Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wata Mota ta ƙaɗe ɗan sandan ne yayin da ya hau Mashin ɗin yan kasuwa wanda mutane suka fi sani da 'Acaɓa' a Eyenkorin, yankin da ke gefen Ilorin, babban birnin jihar ranar Talata.

Kara karanta wannan

2023: Ka mutunta alƙawarin da ka ɗauka, Jigon APC ga Gwamnan PDP da ake raɗe-raɗin zai sauya sheƙa

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar haɗarin da kuma rasuwar babban jami'in ɗan sandan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ajayi ya bayyana cewa Mamacin ya hau Acaɓa a wannan mummunan ranar ne saboda motarsa ta samu matsala ya kai ta Gareji domin gyara.

Sama da shekaru 20 yana wa ƙasa aiki

Da yake tsokaci kan rasuwar jami'in, wani ɗan sanda da ya yi ritaya, Alhaji Ibrahim Ajia, ya ce marigayin, wanda mamba ne a kwas 20/2000, ya kwashe sama da shekara 22 yana yi wa ƙasa aiki.

Daily Trust ta rahoto Ya ce:

"Na kaɗu da jin labarin mutuwar farat ɗaya ta ACP Abolade Oladigbolu, kafin rasuwarsa shi ne kwamandan yankin Alapa a jihar Kwara. Marigayin ya kasance mamban Kwas 20/2000 ya shafe sama da shekara 22 ya na wa ƙasa aiki"

Kara karanta wannan

Babban ɗa ya daɓa wa mahaifinsa wuƙa har lahira kan saɓanin mallakar gona

"Ina tuna maganar da muka yi da shi ta karshe a wannan rana da safe, dukkan mu mun maida hankali ne kan yadda za'a tsare yankuna biyar da ke ƙarƙashinsa domin mu daƙile garkuwa da mutane wanda ke yaɗuwa a ƙasar nan."
"Ina Addu'a Allah mai girma ya sauƙaƙa wa iyalansa da ya bari,Ameen."

A wani labarin kuma kun ji cewa Babbar Mota ta murkushe Sojojin Najeriya biyu har lahira a Kaduna

Wata babbar Motar kwashe shara a Kaduna ta take Sojojin Najeriya guda biyu kuma sun mutu a kan hanyar Mando.

Wani shaida da haɗarin ya auku a gabansa ya bayyana cewa Sojojin sun bugi rami suka faɗi daga kan Babur, Motar ta bi ta kan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262