Sanatoci sun bai wa Buhari wa'adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro, sun yi barazanar tsige shi

Sanatoci sun bai wa Buhari wa'adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro, sun yi barazanar tsige shi

  • Yan majalisar Dattawa da ke tsagin adawa sun yi barazanar tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan matsalar tsaro
  • Sanatocin jam'iyyun adawan sun ba Buhari wa'adin mako shida ya kawo karshen matasalar tsaron ƙasar nan ko su tsige shi
  • Hakan na zuwa ne biyo bayan yawaitar ayyukan ta'addanci a sassan ƙasar nan, wasu na ganin gwamnati bata yin abinda ya dace

Abuja - Mambobin majalisar dattawa daga jam'iyyun hamayya sun baiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wa'adin mako shida ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.

Channels TV ta ce sun yi barazanar fara bin matakan tsige shugaban ƙasan idan ya gaza shawo kan matsalar tsaro a cikin wa'adin da suka ɗibar masa.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Sanatoci sun bai wa Buhari wa'adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro, sun yi barazanar tsige shi Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda, shi ne ya bayyana matsayar Sanatocin yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dirama ta barke a majalisar Dattawan Najeriya, Sanatoci sun fusata

Hayaniya ta ɓalle a majalisa

Kafin bayyana matsayar su, Sanatocin sun fice daga zauren majalisar ne cikin ɓacin rai biyo bayan kiran a tsige shugaban ƙasa Buhari yayin zaman su na yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Aduda ya ta da batun inda ya bukaci, shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya jagoranci tattauna wa kan halin tsaron da Najeriya ƙe ciki da kuma yuwuwar tsige shugaban ƙasa.

Amma lamarin bai yi wa Sanata Ahmad Lawan, wanda ke jagorantar zaman daɗi ba, kuma nan yake ya yi watsi da bukatar shugaban marasa rinjayen da cewa ba zata saɓu ba.

Cikin ɓacin rai, Sanatocin baki ɗaya jam'iyyun siyasa da ba APC ba suka fice daga zauren majalisar duk da ba'a gama zaman ba, sun fita suna faɗin, "Dole Buhari ya sauka, Lawan ma ya bi sahu."

Wannan shi ne na baya-bayan nan a jerin abubuwan nuna damuwa da ɗai-ɗaikun mutane ke yi da kungiyoyi duba da taɓarɓarewar matsalar tsaro a sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta zaɓi sabon shugaba a majalisar Dattawan Najeriya

A wani labarin kuma Atiku, Gwamna Okowa da Dakta Ayu sun gana da sanatocin jam'iyyar PDP a kokarin ɗinke ɓaraka

Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya fara koƙarin rarrashin mambobin jam'iyya gabanin zaɓen 2023.

A wani babban yunkuri, Atiku da abokin takararsa sun gana da Sanatocin PDP domin shawo kan waɗan da suka fusata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262