'Yan Bindiga Sun Sake Garkuwa da Matar Shugaban Filani a Abuja
- Masu garkuwa da mutane sun shiga har cikin gida, sun yi awon gaba da matar shugaban Fulanin Kwali, Abuja, Habiba Adamu
- Uwar gidan Arɗon Fulanin ta ce lokacin harin Mijin su ba ya gida kuma maharan sun samu shiga gidan ne ta kofar baya
- A watan Fabrairu, maharan sun sace Habiba Adamu, amma suka sako ta saboda ba zata iya tafiya ba saboda tsufa
Abuja - Yan bindiga sun sake yin garkuwa da Habiba Adamu, matar Arɗon Fulani na ƙaramar hukumar Kwali a Abuja, Alhaji Adamu Garba Arɗo, kuma wannan shi ne karo na biyu.
Daily Trust ta ruwaito cewa Matar wacce aka yi garkuwa da ita a Watan Fabrairu amma Yan Bijilanti suka ceto ta, ta sake shiga hannun masu garkuwa tare da wasu kananan yara uku ranar Litinin da daddare.
An bayyana sunayen kananan yaran da yan bindigan suka haɗa da su da, Hafsat, Fatima da kuma namiji ɗaya mai suna Abubakar.
Yan bindiga sun sace su ne awanni 24 bayan an yi garkuwa da wasu ma'aurata, Mista Sunday Odoma Ojarume, da matarsa, Misis Janet Odoma Ojarume, a ƙauyen Sheda, ƙaramar hukumar Kwali.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Uwar gidan Arɗon Fulanin, Ƙhadijat Adamu, ce ta tabbatar da sace abokiyar zamanta da yaran uku ga manema labarai ranar Talata.
Ta bayyana cewa yan bindigan sun farmaki Anguwar Tudan Fulani da ke ƙauyen Yangoji, yankin Kwali da misalin ƙarfe 12:04 na dare.
Ta ce maharan sun samu shiga cikin gidan ne ta kofar bayan ɗakin girki, inda ta ƙara da cewa a baya an taɓa awon gaba da ita amma yan bindiga suka sako ta lokacin da suka fahimci ba zata iya tafiya ba saboda shekaru.
'Yan bindiga sun kai kazamin hari babban birnin jihar arewa, sun sace shugaban jami'an tsaro da yan mata
"Yan bindigan sun kutsa cikin gidan ta kofar baya bayan sun gaza balle babbar kofar gida, daga nan suka shiga ɗakina da ɗakin abokiyar zama ta suka tarwatsa komai suna neman kuɗi," Inji ta.
Ina Ardon Fulanin yake lokacin harin?
Uwar gidan ta ce Maigidansu ba ya nan lokacin da maharan suka shiga, inda ta bayyana cewa yan sanda daga Hedkwatar Kwali sun ziyarci gidan bayan harin.
Bayanai sun nuna cewa Arɗon ya yi tafiya zuwa garin Iddah a jihar Kogi, inda ya je duba garken shanunsa da ke kiyo a can.
Har yanzun kakakin hukumar yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta amsa sakonnin da aka tura mata ba kan harin garkuwan.
A wani labarin kuma Wani mummunan hatsari ya rutsa da Sojojin Najeriya a Kaduna, An rasa rayuka
Wata babbar Motar kwashe shara a Kaduna ta take Sojojin Najeriya guda biyu kuma sun mutu a kan hanyar Mando.
Wani shaida da haɗarin ya auku a gabansa ya bayyana cewa Sojojin sun bugi rami suka faɗi daga kan Babur, Motar ta bi ta kan su.
Asali: Legit.ng