Da duminsa: Wani abu mai fashewa ya tashi a ofishin gwamnatin jihar Kogi
- Wani abu mai fashewa ya tashi a farfajiyar ginin ofishin gwamnatin jihar Kogi dake arewacin Najeriya a ranar Talata
- Lamarin ya faru ne wurin karfe 8:30 na safiyar Talata a Lokoja, babban birnin jihar Kogi yayin da 'yan jarida ke shirin fara aiki
- Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace jami'an rundunar cire bam suna wurin lokacin da abun ya fashe
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kogi - Wani gagarumin karar fashewar abu ya tashi a farfajiyar ofishin sakataren gwamnatin jihar Kogi, Dr. Folashade Arike Ayoade.
Ofishin shi ne kusa da Lugard Street. inda majalisar zartarwar kungiyar 'yan jaridan Najeriya, reshen jihar Kogi yake, jaridar Punch ta ruwaito.
Karar fashewar abun an ji shi wurin karfe 8:30 na safiyar Talata yayin da 'yan jarida suka taru domin shirin ayyukansu na ranar.
A yayin da aka tuntubi kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace, "Eh, abinda ya faru shi ne, an sanar da mu cewa an ajiye wani abu mai kama da bom a farfajiyar kuma da gaggawa na tura rundunar cire bom domin duba abun.
"Tuni abun ya fashe da kansa. Karar fashewa da kuka ji aikin rundunar cire bom din mu ce wadanda suka yi kokarin cire abun ba tare da ya cutar da kowa ba."
Tashin Hankali: Wani Bam ya sake tashi a gidan giya a jihar Kogi, mutane sun mutu
A wani labari na daban, a kalla mutum uku ake fargabar sun rasa rayuwarsu kuma wasu da dama suka jikkata yayin da wani Bam ya tashi a Kabba, jihar Kogi da daren ranar Laraba.
An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU
Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:45 na dare lokacin da mutane ke tsaka holewarsu a wani gidan Giya.
Wata majiya ta bayyana cewa:
"Na ji wata ƙara mai tsananin ƙarfi kuma babu nisa daga inda nake, nan take na nufi wurin dom gane wa idona, na ga gawar mutum uku kwance yayin da waɗan da suka jikkata an kai su Asibiti."
An investigation has also commenced to ascertain what the object was.
Asali: Legit.ng