Gwamna Zulum ya raba miliyan N172m da kayan abinci ga Talakawa 30,436 a Damboa
- Gwamnan jihar Borno ya tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa da masu karamin karfi a yankin Damboa
- Farfesa Babagana Umaru Zulum ya sa ido wajen raba tsabar kudi miliyan N172m da kayayyakin abinci ga mazauna 30,436
- Gwamnan ya kuma gudanar da rangadi domin duba wasu ayyuka a kauyuka kafin ya koma cikin garin Damboa inda ya kwana
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya tallafa wa mutanen da Ambaliya ta shafa da masu ƙaramin karfi a garin Damboa, kudancin jihar Borno, jiya Litinin.
Gwamnan, wanda ya tsara yadda za'a raba kayan rage radadin, ya bayar da miliyan N172m a tsabar kuɗi da kayan abinci ga mazauna 30,436, cikin su har da waɗan da Ambaliya ta shafa.
The Nation ta rahoto cewa wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mashawarci na musamman kan midiya, Malam Isa Gusau, ya raba wa manema labarai a Maiduguri.
Ya ce mazauna 436 ne aka gano sun rasa gidajen su, da kayayyakin su na abinci sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun tabbatar da cewa shugaban ƙaramar hukumar Damboa, Farfesa Adamu Garba Alloma, ya gaya wa gwamnan cewa, "Ambaliyar ta lalata gidaje da dama sakamakon haka iyalai da dama suka rasa muhalli."
Yadda Zulum ya raba tallafin
Gwamna Zulum ya umarci kowane mutum ɗaya daga cikin 436 da Ambaliya ta shafa a ba shi dubu N50,000, buhun tsabar masara, kayan sanya wa da tabarma.
Zulum ya kuma jajantawa mutanen yayin da ya roke su da su guji gina gidaje a kan hanyar ruwa domin kare sake faruwar haka nan gaba.
Bayan mutanen da Ambaliya ta takaita, Zulum ya sa ido wajen raba N5,000 da kaya ga mazauna 30,000, mafi yawan su zawarawa ne da mata masu karamin ƙarfi da magidanta daga ƙauyuka daban-daban.
Gwamnan ya yi rangadi a Hausari, tsohuwar kasuwar Danboa da Kachallaburari tun isar sa Ɗamboa ranar Lahadi da yammaci kafin ya kwana a cikin gari.
A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP ya maida wa Atiku Martani game da samun nasara a zaben 2023
Tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ya ƙosa ya ba da mamaki a babban zaɓen 2023.
Peter Obi, yayin martani ga kalaman Atiku Abubakar na PDP, ya ce dama can rayuwar siyasarsa cike take da abubuwan Al'ajabi.
Asali: Legit.ng