'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Coci A Mahaifar Gwamnan Sokoto
- Miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da wani Fadan cocin Katolika a garin Tambuwal da ke yankin jihar Sakkwato
- Bayanai sun nuna cewa Malamin cocin ya sanar da yan sanda haɗarin da ke shirin faruwa da shi, amma ba su kai masa ɗauki ba
- Daraktan sadarwa na Coci-Cocin Katolika a Sakkawato ya roki a sa Malamin da iyalansa cikin Addu'a
Sokoto - Kwanaki kaɗan bayan ɓinne Malamin Majami'ar Katolika, wanda aka sace kuma aka kashe shi a jihar Kaduna, yan bindiga sun sake garkuwa da wani a Sakkwato.
Wasu miyagun yan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun yi garkuwa da Malamin Coci, Tony Udemezue, wanda ke ƙarƙashin Cocin Ƙatolika na jihar Sakkwato.

Asali: UGC
Jaridar Vanguard ta tabbatar a rahotonta cewa an sace Malamin cocin ne a awannin wayewar garin Litinin a gidansa da ke garin Tambuwal, mahaifar gwamna Aminu Waziri Tambuwal a jihar Sokoto.
Daraktan sadarwa na ƙungiyar Malaman Coci-Cocin Katolika a Sakkwato, Rabaran Fr. Chris Omotosho, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fr. Omotosho ya ce:
"Ɗaya ɗaga cikin Malaman Cocin mu a Tambuwal, jahar Sakkwato, Tony Udemezue, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane a gidansa (mahaifar mai girma gwamnan jihar, Aminu Tambuwal).
"Ba bu wani jami'in hukumar yan sanda guda ɗaya da ya kawo ɗauki awa ɗaya kenan (tun karfe 2:00 na dare, wayewar garin Litinin) duk da ya kira ya sanar da su ta wayar salula kafin a yi awon gaba da shi.".
"Dan Allah mu daure mu jure sanya shi da iyalansa cikin Addu'o'in mu."
An kama hatsabibin mai garkuwa
A wani labarin kuma an kama wani ƙasurgumin mai garkuwa yana ɗaukar ma'aikata zasu sace mahaifin kwamishina a Neja

Kara karanta wannan
Tsautsayi: Kwata ta yi ajalin wani matashi ɗan shekara 25, Ghaddafi Saleh, a Kano
Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da ke shirin sace manyan mutane biyu a jihar.
Yayin bincike, wanda ake zargi Alhaji Bashiru ya amsa cewa yana shirin sace su ne saboda bashin kudin da yake bi.
Asali: Legit.ng