Wani Babban Sarki, Mai Martaba Adekunle Salawudeen, Ya Rasu
- Jihar Oyo ta sake rashin wani babban Basaraken gargajiya, Oba Adekunle Salawudeen na masarautar Aseyin ya rasu
- Bayanai sun nuna cewa wannan rasuwar ta kasance ta huɗu a cikin manyan sarakunan jihar cikin watanni Takwas
- Wata majiya daga gidan Sarautar wacce ta tabbatar da rasuwar basaraken yau Lahadi, ta ce ya yi rashin lafiya na ɗan lokaci kaɗan
Oyo - Babban Basaraken masarautar Aseyin wanda ake kira, 'Aseyin na Aseyin' Mai martaba Adekunle Salawudeen, ya riga mu gidan gaskiya, wata majiya daga cikin iyalan gidan sarautar ta tabbatar da haka ga Premium Times.
Basaraken ya kwanta dama ne ranar Lahadi, kuma ya zama Sarki na hudu da ya rasu cikin manyan sarakunan gargajiya na jihar Oyo cikin watanni Takwas da suka shuɗe.
Tun farko dai, Sarkin Ogbomoso wato Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Ajagungbade Oyewumi, ya rasu a watan Disamba 2021, sai kuma Olubadan na ƙasar Ibadan, Oba Saliu Adetunji, ya mara masa baya a watan Janairu, 2022.
Bayan haka babban baraken Oyo, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya koma ga mahalincinsa a watan Afrilu, 2022.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sahihin bayani kan musabbabin abinda ya faru da Basaraken har ya rasa rayuwarsa ya yi wahala amma abin da jaridar ta tattara daga wata majiya a iyalan gidan sarautan ya nuna cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na ɗan lokaci.
Aseyin wani tsohon gari ne na Yarbawa mai ɗumbin tarihi da ke yankin arewacin jihar Oyo, yana da nisan kilomita 90km tsakanin sa da birnin Ibadan, babban birnin jihar.
Matafiya sun rasa rayuwarsu a Katsina
A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya a Katsina, sun kashe rayuka
Tsagerun yan bindiga sun kai hari kan matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya, sun kashe aƙalla mutum uku.
Wani shaidan da abun ya faru a kan idonsa ya ce maharan sun toshe hanyar, suka kwashi mutanen motoci huɗu.
Asali: Legit.ng