Mutumin Da Ya Ci Amanar Saudiyya Ya Taimakawa Dan Jaridar Amurka Shiga Cikin Makkah Ya Shiga Hannu

Mutumin Da Ya Ci Amanar Saudiyya Ya Taimakawa Dan Jaridar Amurka Shiga Cikin Makkah Ya Shiga Hannu

  • Yan sandan Makkah sun kama wani dan kasar Saudiyya bisa zarginsa da ake yi da cin amana
  • Mutumin ya shiga hannu bayan ya taimaka wajen shigar da wani dan jaridar Amurka wanda ba Musulmi ba garin Makkah
  • Mahukunta a kasar Saudiyya sun ce an shigar da Ba'amurken ne ta hanyar da aka tanada don Musulmai kadai

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Saudiyya - Yan sandan Saudiyya sun tura wani dan kasar zuwa sashin gurfanar da masu laifi bayan zarginsa da hannu wajen shigo da wani dan jaridar Amurka da ba Musulmi ba cikin garin Makkah mai tsarki.

Labarin kamun na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin hukumar Saudiyya ta wallafa a Facebook, a ranar Juma’a, 22 ga watan Yuli.

Dan Amurka
Mutumin Da Ya Ci Amanar Saudiyya Ya Taimakawa Dan Jaridar Amurka Shiga Cikin Makkah Ya Shiga Hannu Hot: Haramain Archive
Asali: Facebook

Sanarwar ta kuma bayyana cewa rundunar yan sandan garin Makkah ta gargadi duk masu zuwa masarautar da su mutunta tare da bin ka’idoji da dokokin da aka shimfida, musamman ma kan Harami da wurare masu tsarki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano

Ta kuma bayyana cewa duk wani abu da ya sabawa hakan za a dauke shi a matsayin laifi wanda ba za a lamunta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, sanarwar ta ce akwai hukunce-hukunce da aka tanada ga duk wanda aka samu ya take dokokin.

Sanarwa ta ce:

“Jami’an tsaron Saudiyya sun kama wani dan kasar kan shigowa da bayar da damar shigar da wani dan jarida da ba musulmi ba, wanda ke dauke da shaidar dan kasa na Amurka cikin babban birnin Makkah.
“Rundunar yan sandan Makkah ta gargadi dukkanin masu zuwa masarautar, kan bukatar mutunta ka’idoji da bin doka, musamman a kan Harami da wurare masu tsarki. Duk wani karya doka irin wannan ana daukarsa a matsayin laifi wanda ba za a lamunta da shi ba, kuma za a yi hukunci a kan wadanda suka aikata shi.”

Alhazan Najeriya sunyi korafi akan yadda ake nuna musu Banbanci a Saudiya

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Sake Kama Wasu Da Suka Tsere Daga Kurkukun Kuje A Jihohin Arewa 2

A wani labari na daban, wasu Mahajjatan Najeriya sunyi korafi akan yadda hukumar kasar Saudiyya ta nuna musu bambanci a zama na Muzdalifa a lokacin aikin Hajjin bana.

Rahoton BBC HAUSA Cikin alhazawan da suka zanta da masu rahoton BBC sun ce akwai bambancin tsakanin Abubwan da hukumar kasar ta tanadar wa mahajjatan Najeriya da wadanda ba yan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng