EFCC Ta Gurfanar Da Dakataccen Akanta Janar Na Tarayya A Gaban Kotu Kan Zambar N109bn
- Tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, ya gurfana a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Idris da wasu biyu a ranar Juma'a, 22 ga watan Yuli, kan wasu tuhume-tuhume 14
- Ana dai zargin dakataccen Akanta Janar na tarayyan da wawure kudi da suka kai naira biliyan 109.5
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta isa babbar kotun tarayya tare da dakataccen Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, jaridar The Cable ta rahoto.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon Akanta Janar din da wasu biyu sun gurfana a gaban kotun da ke Abuja a yau Juma’a, 22 ga watan Yuli.
A watan Mayu ne aka kama Idris a Kano bayan ya ki amsa gayyatar da hukumar ta yi masa don amsa tambayoyi kan zargin wawure kudi har naira biliyan 80
Kwanaki biyu bayan kama tsohon Akanta Janar din, sai ministar kudi, Zainab Ahmed ta dakatar da shi har sai baba ta gani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sanya ran za a gurfanar da Idris tare da Godfrey Olusegun Akindele da Mohammed Kudu Usman, yayin da aka kuma ambaci sunan kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited a cikin tuhumar.
Hukumar EFCC ta ce ana zargin Idris da sauran wadanda ake kara a kan wasu tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata da cin amana wanda ya kai Naira biliyan 109.5.
Tsohon AGF Ya Karɓi Biliyan N15bn Don Gaggauta Biyan Jihohin Ɗanyen Mai Kuɗaɗensu, EFCC
A gefe guda, mun ji cewa Akanta Janar na ƙasa (AGF) da aka dakatar, Ahmed Idris, ya karɓi biliyan N15bn ta bayan fage domin ya gaggauta biyan jihohi masu fitar da ɗanyen mai kason da ake ware musu.
Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'adi (EFCC) ta ce dakataccen AGF ɗin ya karɓi kudin ne a matsayin toshiyar baki domin saurin tura wa jihohin guda 9 ƙaso 13% da ake ware musu.
Daily Trust ta ruwaito cewa ƙaso 13% na kuɗaɗen da aka samu wata garabasa ce da tsarin rabo ya ware domin taimaka wa yankunan da ake haƙo ɗanyen mai su cigaba.
Asali: Legit.ng