'Ba zan taɓa manta wa ba' Mahaifiyar Deborah Samuel da aka kashe a Sokoto kan zagin Annabi

'Ba zan taɓa manta wa ba' Mahaifiyar Deborah Samuel da aka kashe a Sokoto kan zagin Annabi

  • Mahaifiyar ɗalibar makarantar Kwaleji ta Shehu Shagari, Deborah Samuel, wacce aka kashe da zargin ɓatanci ta faɗi halin da ta shiga
  • Matar mai suna, Alheri Emmanuel, ta ce ta samu labarin kisan ɗiyarta ta bakin ƙawayenta kuma ba zata taɓa mance wa da ranar ba
  • Fusatattun matasa sun kashe Deborah ne bayan ta yi wasu munanan kalamai da zagi ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Alheri Emmanuel, mahaifiyar Deborah Samuel, Ɗalibar kwalejin ilimi ta tunawa da Shehu Shagari dake Sakkwato, wacce aka kashe bisa zargin ɓatanci, ta bayyana yadda labarin kisan ɗiyarta ya zo kunnenta.

Alheri ta bayyana halin da ta shiga ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, inda ta ce ta samu labarin kashe ɗiyarta ne ta bakin ƙawar Deborah.

Deborah Samuel.
'Ba zan taɓa manta wa ba' Mahaifiyar Deborah Samuel da aka kashe a Sokoto kan zagin Annabi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mahaifiyar, wacce ta fashe da kuka yayin da take hirar, ta bayyana cewa ba zata taɓa mance wa da wannan ranar ba a rayuwarta.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankaɗo yadda Dakataccen Akanta Janar ya karɓi Biliyan N15bn na goro don saurin biyan jihohi 9 wasu kuɗaɗe

Waya faɗa wa Alheri abinda ya faru?

A ruwayar Daily Trust, Alheri ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ranar da wannan mummunan labarin ya faru naji tamkar an soke ni, ɗaya daga cikin ƙawayenta ta kira ni ta wayar salula. Tun kamin ta faɗa mun naji suna kuka, ta ce Mama sun yi alƙawarin sai sun kashe Deborah."
"Bayan wani lokaci sai maƙotan mu da yan uwa suka fara zuwa jajanta mana. Wata ƙawarta ta daban ta sake kira na, ta ce Mama sun kashe Deborah."

Kisan Deborah ya haddasa zazzafar muhawara a sassan ƙasar nan baki ɗaya, inda wasu yan Najeriya suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciko waɗan da suka aikata wannan babban laifin.

Matasa kuma ɗaliban makarantar kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari sun kashe Deborah ne bayan ta yi kalamai munana har da zagi ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kwata ta yi ajalin wani matashi ɗan shekara 25, Ghaddafi Saleh, a Kano

Bayan faruwar wannan lamari, hukumar yan sanda a Sakkwato ta sanar da cewa ta kama wasu da take zargin suna da hannu a kisan, lamarin ya haifar da zanga-zanga a sassan jihar Sakkawato.

A wani labarin kuma kun ji cewa Abba Kyari ya faɗi Yadda ya tsallake rijiya da baya lokacin harin yan ta'adda a Kuje

Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, ya ce ya ɓuya kamar ɓera lokacin harin yan ta'adda a Kuje.

A zaman Kotu na yau Laraba, Kyari ta bakin lauyansa ya sake shigar da bukatar beli, ya ce ya samu damar tsere wa amma ya ƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: