Yanzu-yanzu : Abduljabbar Nasiru Kabara Ya Nemi A Sauya Masa Kotu

Yanzu-yanzu : Abduljabbar Nasiru Kabara Ya Nemi A Sauya Masa Kotu

  • Malam Abduljabbar ya nemi Shugaban Alkalai na Jihar Kano, Dokta Tijjani Yusuf Yakasai ya sauya masa kotun da ke sauraren shari’arsa
  • Abduljabar Nasiru ya zargi Alkali Ibrahim Sarki Yola, da hana shi damar kare kansa yadda ya kamata
  • Abduljabar yace bai gamsu da yadda shari’ar sa ke tafiya da kuma mu’amalar da alkali ke yi da bangarorin da suka shigar da karar sa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Babban malamin da ake zargi da yiwa Annabi batanci, Abduljabbar Nasiru kabara ya nemi a canza masa kotun dake sauraren karar sa kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Abduljabar ya nemi Shugaban Alkalan jihar Kano, Dokta Tijjani Yusuf Yakasai ya sauya masa kotun ne saboda zargin rashin ba shi damar kare kansa yadda ya kamata da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke yi.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa mu ka ba ‘Dan bindiga sarautar Sarkin Fulani inji Masarautar Yandoto

Abduljabbar Nasiru Kabbara wanda jigo ne a Darikar Kadiriya ya bayyana hakan ne a zaman kotun da aka yi a yau ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.

Kabara
Yanzu-yanzu : Abduljabbar Nasiru Kabara Ya Nemi A Sauya Masa Kotu FOTO BBC
Asali: Facebook

Shehin Malamin ya gabatar da bukatan sa ne bayan da kotun ta nemi sanin dalilin da ya hana lauyansa halartar zaman kotun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayani, Abduljabbar ya shaida wa kotun cewa ya rubuta wa Shugaban Alkalan Jihar takardar neman a sauya masa kotu saboda rashin gamsuwarsa da yadda shari’ar ke tafiya da yadda alkalin kotun ke mu’amala da bangarorin da suka shigar da karar sa.

Karin bayani na tafe.

Abduljabbar Kabara ya shigar da karar Gwamnatin jihar Kano a gaban babban kotu

A wani labarin kuma, Babban kotun tarayya da ke zama a garin Kano, ya tsaida ranar da za a kuma sauraren karar da Lauyan shehin malami, Abduljabbar Kabara ya shigar.

Jaridar Sun ta kasar nan ta ce Sheikh Abduljabbar Kabara ya kai karar gwamnatin jihar Kano a kotu ta hannun wani lauyansa mai suna Dalhatu Shehu-Usman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel