Gwamnan Ondo ya umarci a kori ma'aikatan dake karɓan Albashi biyu
- Gwamnan Ondo ya umarci shugaban ma'aikatan jihar ya sallami duk wanda aka gano yana karɓan albashi fiye da ɗaya
- Rotimi Akeredolu (SAN) ya ce nauyin ma'aikata ya zarce ƙima a jerin waɗan da ake biya albashi duk wata haɗi da yan fansho
- Kwamitin da gwamnan ya kafa domin gudanar da bincike da bin kwakkwafi kan ma'aikatan da ake biya kuɗi ya miƙa rahotonsa
Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, SAN, ya umarci shugaban ma'aikata ta rubuta takardar sallama ga duk jami'in gwamnati da aka gano yana karɓan Albashi fiye da ɗaya.
Daily Trust ta ce gwamnan ya ba da wannan umarnin ne yayin da ya karɓi rahoton kwamitin bincike, bin ƙwakkwafi da sharar jerin ma'aikatan da ake biya Albashi.
Gwamnan, wanda ya zargi cewa tsarin da ya haɗa da masu karɓan albashi da Fansho an gurɓata shi, ya kafa kwamitin mutum Bakwai domin su bincika ma'aikatan da ke tsarin.
Kwamitin bisa jagorancin tsohon Sakataren dindindin na ma'aikatar kuɗi, Mista Victor Olajorin, ya miƙa rahoton binciken da ya gudanar ga gwamnan a Ofishinsa, Alagbaka, Akure.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake karɓan rahoton, Gwamna Akeredolu ya jijjiga da ganin abubuwan da aka bankaɗo kuma ya koka da nauyin ma'aikata fiye da ƙima, wanda a cewarsa ke tattare da ma'ikatan bogi.
A kori duk wanda ke karɓan Albashi sama da ɗaya - Akeredolu
Daga nan sai gwamnan ya umarci ma'aikatu, hukumomi da sashi-sashin gwamnatin jiha (MDAs) su dakatar da ɗaukar ma'aikata ƙarƙashin kowaye har sai kwamitin ya kammala aikinsa.
"Muna da nauyin ma'aikata fiye da ƙima, wanda babu tantama ina da tabbacin ƙunshe suke da ma'aikatan bogi."
"Duk masu karɓan albashi fiye da ɗaya, bayan kwato kuɗaɗen, ina ba shugaban ma'aikata umarnin ya kore su, ya zama wajibi su zama izini ga saura," inji gwamnan.
Tun da farko, shugaban kwamitin Olajorin, ya gaya hanyoyin da gwamnonin suka bi wanda ya haɗa da tuntuɓar kowace hukuma, inda suka samu muhimman abubuwa kamar ma'aikatan da aka ɗauka, rijistar biyan albashi, fansho da sauran su.
A bayanansa, ya shaida wa gwamnan cewa sun gano gwamnati ta yi asarar kuɗi sama da miliyam N400m tun zuwansa kan madafun iko, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya
A wasu lokutan Gwamnonin da ke kan madafun iko kan rasa damar tazarce a Najeriya, a baya-bayan nan mutane sun shaida yadda karfin mulki ya gaza a zaɓen Osun da aka kammala.
Wasu gwamnoni a Najeriya sun sha kaye yayin da suka yi yunkurin ganin sun zarce zango na biyu a kan kujerun su a lokuta daban-daban.
Asali: Legit.ng