'Dan majalisa na zargin mai magana da yawun majalisar wakilai da neman matarsa

'Dan majalisa na zargin mai magana da yawun majalisar wakilai da neman matarsa

  • Tsohon 'dan majalisar wakilan Najeriya, Robinson Uwak, ya jaddada cewa mai magana da yawun majalisar, Benjamin Kalu, yana neman matarsa suna lalata
  • Uwak ya kara da zargin 'dan majalisar da hada baki da matarsa wacce suke da 'ya'ya biyu da ita da ta saka masa guba a abinci kuma ta kashe shi
  • Ya sanar da hakan ne yayin martani ga wata takarda da Kalu ya fitar ta hannun lauyansa inda ya bukaci ya janye maganarsa kuma ya bashi hakuri kan zargin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Robinson Uwak, tsohon 'dan majalisar wakilai ya jaddada cewa mai magana da yawun majalisar wakilai, Benjamin Kalu, yana da wata alakar cin aman da matarsa mai suna Keiza Uwak.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Uwak yayin martani ga wasika mai kwanan wata 17 ga Yulin 2022, ta hannun lauyansa, inda Kalu ya bukaci ya janye wannan mummunan zargin tare da bashi hakuri.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

'Yan majalisa
'Dan majalisa na zargin mai magana da yawun majalisar wakilai da neman matarsa. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

Tsohon 'dan majalisar ya jaddada cewa, a cikin batunsa babu kokwanto kuma ba kirkirarren zance bane ko karya.

Mai Magana da yawun majalisar wakilai ya karyata

Mai magana da yawun majalisar wakilan Najeriya, Kalu Benjamin, yace wannan zargin ba zai girgiza shi ba inda ya kwatanta shi da maras tushe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da jaddada cewa, aiwatarwa tare da isar da mulki wanda mazabarsa zata kurba daga romon damokaradiyya ne abinda ya saka a gaba.

Kalu ya kara da cewa, bai taba haduwa da Uwak ba a baya kuma bai yi magana da matarsa ba tun bayan da ya bar majalisar a 2009.

Ka hada baki da matata ku saka min guba in ci in sheka lahira, 'Dan majalisa ya zargi Kalu

A martanin Uwak, ya jaddada cewa zargin da yake masa duk gaskiya ne inda ya kara da cewa, ya hada baki da matarsa wacce suke da 'ya'ya biyu da ta saka masa guba a binci.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

"Na kara sanar da cewa, wadannan kalaman kan Benjamin Kalu ba karya bane kuma ba kirkiro su nayi ba. Gaskiya ne kuma sun fito daga bakin mutum ne wanda ke son tseratar da rayuwarsa tare da aurensa."

Bidiyo: Dangote ya halarci nadin sarautar matar marigayi Abba Kyari matsayin Gimbiyar Jama'are

A wani labari na daban, Sarkin Jama'are, Mai martaba Alhaji Nuhu Wabi III, ya nada matar marigayi tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu a matsayin gimbiyar farko ta Jama'are.

A bikin nadin sarautar da aka yi a fadarsa ranar Lahadi, sarkin ya kwatanta ta da diya tagari a Jama'are wacce ta yi matukar kokari wurin kawo cigaba ga dukkan masarautar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng