Na ɓuya tamkar ɓera yayin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya faɗa wa Kotu

Na ɓuya tamkar ɓera yayin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya faɗa wa Kotu

  • Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, ya ce ya ɓuya kamar ɓera lokacin harin yan ta'adda a Kuje
  • A zaman Kotu na yau Laraba, Kyari ta bakin lauyansa ya sake shigar da bukatar beli, ya ce ya samu damar tsere wa amma ya ƙi
  • A ranar 5 ga watan Yuli, yan ta'adda suka kai hari gidan Yarin Kuje, inda suka kwance fursunoni sama da 500

Abuja - Mataimakin kwamishinan yan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari, ya ce ya ɓuya kamar ɓera lokacin da aka kai hari gidan Yarin Kuje da ke birnin tarayya Abuja.

The Cable ta ruwaito cewa a ranar 5 ga watan Yuli, 2022, yan ta'adda suka kai farmaki gidan Yarin Kuje, inda suka buɗe Fursunoni sama da 500. ciki har da mayaƙan Boko Haram da ke tsare.

Kara karanta wannan

2023: Hukuncin tsawon rayuwa da INEC take son a yi wa yan siyasa masu siyan kuri'u a Najeriya

Duk da raɗe-raɗin cewa jarumin ɗan sanda Abba Kyari, da wasu manyan mutane sun tsere, mai magana da yawun hukumar gidajen gyaran hali (NCoS), Abubakar Usman, ya ƙaryata rahoton.

Yadda yan ta'adda suka farmaki Kuje.
Na ɓuya tamkar ɓera yayin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya faɗa wa Kotu Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Da yake ƙara shigar da bukatar beli a zaman Kotu na yau Laraba, Kyari ta bakin lauyansa, Onyechi Ikpeazu, ya ce ya samu cikakkiyar damar guduwa amma ya ƙi amfani da ita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce harin da aka kai wa wurin ya kara 'Samar da yanayi na musamman' da zai ba Kotu damar ba da belin shi da sauran waɗan da ake zargi, kafin gama shari'a kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi.

Lauyan Abba Kyari ya ce:

"Mai shari'a duk wani mai rai da ke rayuwa a ƙasar nan zai amince cewa ba wai fashin magarƙama ba, wani mummunan hari ƙungiyar ta'addanci ta kai, ba wai nasarar fasa gidan Yarin kuje kaɗai suka yi ba, sun kwace iko da shi na sama da awanni uku."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai kazamin hari jihar Katsina da tsakar rana, sun aikata mummunar ɓarna

"Duk da haka wanda ake zargi, kasancewarsa ɗan ƙasa mai bin doka sau da kafa, bai gudu ba, idar har akwai wata hujja da zata nuna wanda ake zargi ba zai tsallake beli ba to wannan yanayin ne. Kofar wurin an barta a buɗe na awa uku."
"A taƙaice ma wanda ake ƙara (Abba Kyari) ɓoye wa ya yi kamar ɓera sabida ƙungiyar da ta kai harin ta shiga ɗaki ɗaki tana faɗin zata ɗauke shi da sauran fursunoni su tsere."

Lauyan ya ƙara da cewa waɗan da ake ƙara sun yi tsammanin za'a iya farmakan wurin, wanda hakan ya sa suka nemi Beli tun farko amma aka hana su, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wane mataki Kotu ta ɗauka kan batun Belin?

Alkalin da ke jagorantar shari'ar, Mai shari'a Emeka Nwite, ya ɗage yanke hukunci kan sabuwar buƙatar belin zuwa ranar 30 ga watan Agusta, 2022.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban jam'iyyar APC a jiha, yan sanda sun ce ba zata saɓu ba

A wani labarin kuma An fara shari'ar Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida mai karfi a Kotu

NDLEA ta buɗe shari'ar dakataccen mataimakin kwamishina, Abba Kyari, kan tuhumar safarar miyagun kwayoyin a babbar Kotun tarayya.

Hukumar ta gabatar da shaida a zaman jiya Litinin, kuma Kotu ta karɓa ba tare da jayayya ba daga ɓangaren Kyari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262