Yanzu-yanzu : Wutan Lantarkin Najeriya ya sake lalacewa
- Hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta gamu da koma bayan wutan lantarki a yau Laraba 7
- Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Eko ta tabbatar da ruftawar wutar lantarkin Najeriya a safiyar ranar Laraba
- Kamfanonin rarraba wutar sun koka akan rashin samun kudaden shiga wajen gudanar da ayyukan su yadda yakamata
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta gamu da koma bayan wutan lantarki a yau Laraba 7 ga Watan Yuli 2022. Rahoton THE NATION
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Eko ta tabbatar da ruftawar wutar lantarkin da misalin karfe 11:27 na safe.
“Ya ku abokan ciniki, muna nadamar sanar da ku rahoton rugujewar wutar lantarkin Najeriya da misalin karfe 11:27 na safiyar yau Laraba, 20 ga watan Yuli.
“Muna tattaunawa da Kamfanin Watsa wuta lantarkin Najeriya (TCN) domin gano musabbabin rugujewar wutar dan shawo kan matsalar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamfanin Disco ta bayyana haka ne a shafin ta na Twitter a ranar Laraba.
Watanni uku da suka gabata Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kamfanonin rarraba wutar sun koka kan rashin samun kudaden shigar da ake samu wajen samar da iskar gas da kuma al’amuran fasaha da galibin sassan masana’antun da ake harba iskar gas da aka ce suna karkashin kulawa.
Abin da bincike ya bayyana game da Abba Kyari da Sauransu, Shaidan NDLEA
A wani labari kuma, Wani shaida a shari’ar da ake yi wa dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Abba Kyari, ya ce gwajin da aka yi wa sinadarin da aka gano a hannun Abba Kyari, ya nuna cewa hodar iblis ce. Rahoton PREMIUM TIMES
Kyari da wasu mutane hudu da suka hada da ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insifeto Simon Agirigba , da John Nuhu sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja kan zargin badakalar miyagun kwayoyi
Asali: Legit.ng