An fara shari'ar Abba Kyari kan safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida

An fara shari'ar Abba Kyari kan safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida

  • NDLEA ta buɗe shari'ar dakataccen mataimakin kwamishina, Abba Kyari, kan tuhumar safarar miyagun kwayoyin a babbar Kotun tarayya
  • Hukumar ta gabatar da shaida a zaman jiya Litinin, kuma Kotu ta karɓa ba tare da jayayya ba daga ɓangaren Kyari ba
  • An kama fitaccen jami'in hukumar yan sandan ne bisa zargin hannu a safarar miyagun kwayoyi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA ta buɗe shari'a da dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi a babbar kotun tarayya, Abuja.

Hukumar ta gabatar da kwamandan miyagun kwayoyi (sashin bincike), Patricia Afolabi, domin ta ba da shaida ta farko a gaban mai shari'a Emeka Nwitw, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shaidar ta faɗa wa Kotu cewa aikinta a hukumar NDLEA ya ƙunshi karba da kuma gudanar da bincike kan abubuwan da suka shafi miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na cikin koshin lafiya, in ji Mai magana da yawunsa

Abba Kyari.
An fara shari'ar Abba Kyari kan safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ta sanar da Kotu cewa a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2022, jami'in hukumar, Abubakar Aliyu, ya kawo mata wani Fakiti da ake ganin abun da ke ciki ɗauke da kulli 24 a ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da ta yi wa Kotu, ta ce kowane ƙulli na dauke da wani abu fari mai nauyin giram 0.5grams, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Shaidar ta ƙara da zayyana wa Kotun cewa fakitin da aka kawo mata ya kunshi takarda wato Fom ɗin bukatar gudanar da bincike kan abubuwan da ke ciki.

Me binciken ya bankaɗo?

Shaidar ta ce:

"Daga binciken da na gudanar wanda na raɗa wa, 'Exhibits A-X' ma gano cewa 21 daga cikin kullin abubuwan da aka kawo mun na ɗauke da hodar iblis, yayin da sauran abubuwan H zuwa G ba bu komai a ciki."

Kara karanta wannan

Auren manya: Ana babban shiri, dan tsohon shugaban kasa 'Yar Adua zan angwance

"Daga nan sai na kai rahoton abun da bincike na ya tabbatar, wanda na sa hannu kuma na buga hatimi, na sake sanya su a fakitin Anbulaf na tura adireshin O.C na NDLEA Abuja."

Daga nan Kotun ta amince da dukkan abubuwan da aka gabatar a matsayin shaida ba tare da jayayya daga ɓangaren masu kariya ba.

Abinda ɓangaren Abba Kyari suka yi

Yayin tambayoyi ga shaida, Lauyan wanda ake zargi, Onyechi Ikpeazu (SAN), ya tambayi shaidar cewa shin gaskiya ne cewa duk wanda ake tuhuma a harƙallar kwayoyi dole ya hallara kafin gudanar da binciken kayan? Ta amsa da a'a.

Shaidar ta ba shi amsa da cewa ba dole bane duk wanda ake tuhuma ya kasance a wurin yayin da za'a gabatar da kaya masu alaƙa da shi domin gudanar da bincike.

Afolabi, wacce ta bayyana cewa tana da kwarewar aiki na shekara 30, ta ƙara da bayanin cewa, "Bana wurin lokacin da aka kama kwayoyin. Kuma bana nan lokacin da aka miƙa wa NDLEA."

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka sha ƙasa a zaɓe yayin da suka yi yunƙurin tazarce kan kujerun su a Najeriya

Ta kuma tabbatar da cewa jami'an hukumar NDLEA na nan girke a kowace hanyar shigowa Najeriya, wanda ya haɗa da filin jirgin sama na Akanu Ibiam dake Enugu.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a birnin Shehu ta ce babu ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya.

Da take yanke hukunci, ta tabbatar da hukuncin farko da babbar Kotun tarayya ta Gusau ta yanke kan gwamna Bello Matawalle.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262