Daga karshe, shugaban Hukumar Kiyaye Hadura FRSC Boboye Oyeyemi yayi ritaya daga aiki

Daga karshe, shugaban Hukumar Kiyaye Hadura FRSC Boboye Oyeyemi yayi ritaya daga aiki

  • Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa watau Federal Road Safety Comission (FRSC), Boboye Oyeyemi, ya yi ritaya daga aiki
  • Boboye Oyeyemi yana daya daga cikin tsirarun jami’an da suka kafa hukumar Federal Road Safety Comission FRSC a Najeriya
  • Oyeyemi yayi Ritaya shekaru takwas bayan da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi a matsayin shugaban FRSC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

ABUJA – Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa Federal Road Safety Comission (FRSC), Boboye Oyeyemi, ya yi ritaya daga aiki. Rahoton INDEPENDENT

Ranar Juma'a 19 Yuni za a mishi Faretin fita daga aiki (Pull Out Parade) a Abuja kafin a sanar da wanda zai maye gurbin sa.

Oyeyemi yayi ritaya shekaru takwas bayan da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya nada shi a matsayin Corps Marshal a ranar 23 ga Yuli, 2014.

Kara karanta wannan

Auren manya: Ana babban shiri, dan tsohon shugaban kasa 'Yar Adua zan angwance

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in kula da hulda da jama’a na hukumar Federal Road Safety Comission, FRSC Bisi Kazeem ya fitar.

Oyeyemi
Shugaban Hukumar Road Safety Boboye Oyeyemi yayi ritaya daga aiki FOTO INDEPENDENT
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyeyemi wanda yana daya daga cikin tsirarun jami’an da suka kafa hukumar Federal Road Safety Comission FRSC, ya yi aiki a dukkanin manyan ma’aikatun hukumar, kuma ya yi fice wajen gudanar da aikin sa yadda ya kamata.

Cikin kudurin sa Oyeyemi Boboye, ya magance matsalar rashin matsuguni na ofis wanda yawancin jihohi haya hukumar take yi. Ya tabbatar da an gina ofis na din-din a duka shiyoyin kasar.

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

A wani labari kuma, Plateau - Tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Victor Dimka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2023.

Dimka, wanda ya kasance tsohon kwanturolan hukumar kwastam a wata hira da manema labarai a garin Jos, ya ce Tinubu dan siyasa ne da ya yarda da hadin kai da ci gaban Najeriya a matsayin kasa daya, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Tags: