Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin Oyo ta amince da Bayo Lawal a matsayin sabon mataimakin gwamna
- Yan sa'o'i kadan bayan tsige Rauf Olaniyan daga kujerar mataimakin gwamnan jihar Oyo, an maye gurbinsa da Adebayo Lawal
- Kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Adebo Ogundoyin, ne ya karanto wasikar da Gwamna Seyi Makinde ya aike majalisar na neman a tabbatar da nadin Lawal
- A yau Litinin, 18 ga watan Yuli ne dai majalisar ta tsige Olaniyan bayan ta same shi da aikata laifukan da ake tuhumarsa a kai
Oyo - Majalisar dokokin jihar Oyo a ranar Litinin, 18 ga watan Yuli, ta amince da nadin Adebayo Lawal a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar bayan tsige Rauf Olaniyan, jaridar Punch ta rahoto.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan Gwamna Seyi Makinde ya gabatarwa yan majalisar sunan Lawal domin tantance shi a matsayin wanda zai maye gurbin Olaniyan.
Nigerian Tribune ta rahoto cewa kakakin majalisar, Hon. Adebo Ogundoyin, ne ya karanto wasikar da Gwamna Seyi ya aike majalisar a zamansu na yau Litinin.
Kafin nadin nasa, Lawal ya kasance shugaban kamfanin gidaje na jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma yi aiki a matsayin babban Atoni Janar na jihar.
An tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo daga kan kujerarsa
A baya mun kawo cewa an tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo, Mista Rauf Olaniyan, daga kan kujerarsa.
Nigerian Tribune ta rahoto cewa an tsige Olaniyan ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da rahoton kwamitin mutum bakwai da babban alkalin kotu ya kafa don binciken zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan na rashin da’a a zamanta na ranar Litinin.
Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Oyo, Sanjo Adedoyin, ya ce an samu mataimakin gwamnan da dukka laifukan da ake zarginsa a kai.
Asali: Legit.ng