2023: Hukumar zaɓe INEC ta ƙara wa'adin yin katin zaɓe zuwa 31 ga wata
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙara wa'adin cigaba da rijistar masu kada kuri'a har zuwa 31 ga watan Yuli, 2022
- Hakan ya biyo bayan kawo ƙarshen shar'ar da take yi da SERAP, wacce Kotun tarayya ta yi watsi da ita
- INEC ta ce ta ƙara yawan awanni da ma'aikata zasu yi aiki kana ta ƙara ranaku zuwa kowace rana maimakon ranakun aiki
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ƙarin lokacin cigaba da yin rijistar masu kaɗa kuri'a (CVR) zai ƙare ranar 31 ga watan Yuli, 2022.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da babbar Kotun tarayya ta yanke ranar Laraba. wanda ta yi watsi da ƙarar kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) wacce ta nemi a ƙara wa'adin ya zarce 30 ga watan Yuni.
Jam'iyyar APC ta samu gagarumin goyon baya ana dab da zaɓe, wata jam'iyyar adawa ta koma bayan ɗan takararta
INEC ta bayyana da haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin watsa labarai da ilimantar da mutane, Festus Okoye, da ta sanya shafinta na Tuwita.
A sanarwan, Okoye ya ce Kotu ta yanke cewa INEC na da yancin zaɓen ranar da zata dakatar rijistar masu zaɓe, matukar bai shiga kwanaki 90 na ƙarshe kafin ranar babban zaɓe kamar yadda kundin zaɓe 2022 ya tanada.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Domin biyayya ga umarnin Kotu na tsakiyar shari'a kafin yanke hukunci kan ƙarar da kuma ba mutane damar cigaba da rijista, hukumar ta cigaba da aikin rijistar har bayan 30 ga watan Yuni, 2022."
"Bisa wannan dalilin tuni muka ƙara wa'adin CVR zuwa bayan 30 ga watan da kwana 15. Bayan yanke hukuncin babbar Kotun tarayya, dukkan damuwowin da suka shafi shari'a sun warware."
"Saboda haka, daga yanzu an ƙara wa'adin rijista da mako biyu zuwa 31 ga watan Yuli, 2022, wanda da haka adadin lokacin da aka ƙara ya kai kwana 31 (1-31 ga watan Yuli."
INEC ta ƙara awanni da ranaku
Kwamishinan ya ƙara da cewa INEC ta ƙara awannin aikin kowace rana zuwa awanni Takwas, maimakon 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana ya koma 9:00 na safe zuwa 5:00 na yamma.
Haka nan Okoye ya ce an ƙara ranakun gudanar da aikin har da Asabar da Lahadi maimakon a baya da ake aikin a ranakun mako kaɗai.
A wani labarin kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle zuwa APC
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a birnin Shehu ta ce babu ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
Da take yanke hukunci, ta tabbatar da hukuncin farko da babbar Kotun tarayya ta Gusau ta yanke kan gwamna Bello Matawalle.
Asali: Legit.ng