Yadda Ɗan Acaɓa ya yi sanadin ceton ɗan shekara uku daga hannun masu garkuwa

Yadda Ɗan Acaɓa ya yi sanadin ceton ɗan shekara uku daga hannun masu garkuwa

  • Wani ɗan Acaɓa ya taimaka wajen fallasa asirin wata mai garkuwa da mutane bayan ya yi kurkure kaɗe ta da Mashin a Ondo
  • Matashiyar yar shekara 23 ta shiga hannu bayan ta ɗakko jaririn wata mata da nufin guduwa kuma ta yi hatsari garin tsallaka titi
  • Tuni dakarun yan sanda suka damƙe ta zuwa Ofishin su, sun samu wayar Android da wani Bokiti a tare da ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ondo - Wata budurwa mai satar mutane yar shekara 23, Aanu Afolabi, ta shiga hannun dakarun yan sanda bisa zargin yunkurin garkuwa da wani jariri ɗan shekara Uku a yankin lkare Akoko, jihar Ondo.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa mahaifiyar jaririn, Misis Bamitale, ta barshi a shago domin zuwa ɗakko wasu kayayyakin amfani na gida a wani shago da ke layi na gaba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyoyin Naira na fansar Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka rage

Taswirar jahar Ondo.
Yadda Ɗan Acaɓa ya yi sanadin ceton ɗan shekara uku daga hannun masu garkuwa Hoto: punchng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa kafin ta dawo, wacce ake zargin ta shiga shagon ta ɗauki jaririn ta goya shi cikin sauri-sauri ta kama hanyar tsere wa.

Wane kokari ɗan Acaɓa ya yi?

Sai dai wani ɗan Acaɓa ya yi kuskuren kaɗe ta da Mashin ɗinsa yayin da take saurin tsallaka titi da jaririn da ta sato.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya da abun ya faru a gabanta, ta ce:

"Lokacin da Ɗan Acaɓa da wasu mutane da ke kusa suka yi sauri don taimaka mata da yaron da take goye da shi, nan ne fa ɗaya daga cikin mutanen da suka kawo ɗauki ta gane jaririn, ta rutsa ta da tambayoyi."
"Da aka tambayeta sunan jaririn da take goye da shi sai bakinta ya fara rawa ta gaza ba da cikakkiyar amsa. Mai taimakon ta faɗa wa saura cewa ta san yaron da mahaifiyar shi, a takaice ma makotanta ne."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

"Daga nan sai suka nemi ɗauki, suka kira mahaifiyar jaririn da kuma yan sanda, waɗan da suka kama matar suka tafi da ita caji Ofis domin amsa tambayoyi."

Wane matakin yan sanda suka ɗauka kan matar?

Yayin da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Ondo, Funmi Odunlami, ya tabbatar da kama matar da ake zargin da cewa, "Mun sami matar da wayar Android da wani bokiti."

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Rikicin APC ya kara ƙamari bayan zaɓo mataimakin Tinubu, wani babban ƙusa ya fice daga jam'iyyar

Batun zaɓo Musulmi a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya bar baya da ƙura a cikin jam'iyyar.

Tsohon shugaban hukumar soji ta ƙasa kuma babban ƙusa a APC, AVM Frank Ajobena, ya sanar da fita daga jam'iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262