Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

  • Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Bimbo Akinsanya, tace har a yanzu da take shekaru 52 bata ga nagartaccen namijin da ya dace da ita ba
  • A cewarta, matukar zata yi aure, tun a yayin soyayya zata lura da idon basira kan saurayin da kuma danginsa, don ba kowa bane ke da tarbiya tagari
  • Ta bayyana cewa, cin zarafi ne ya koro ta daga gidan tsohon mijinta da yaro jinjiri mai watanni uku, wanda a yanzu ita kadai ke kula da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitacciyar jarumar masana'antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure.

A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta bai wa 'danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kwastoma ya sharɓawa karuwa wuƙa bayan ta ƙi karbar N1,000 na 'aikinta'

Bimbo Akinsanya
Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52. Hoto daga madailygist
Asali: UGC

Ta bayyana yadda take kula da 'danta ita kadai ba tare da tallafin uban yaron ba.

"Ba abun wasa bane kula da 'da kai kadai babu wani tallafi. Tunda na rabu da mahaifinsa, ban taba samun wani tallafi na kula da yaron ba har yanzu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangaren batun aure kuwa, tace: "Ban taba nadamar rabuwa da mahaifin 'da na ba. Barin gidan aure da yaro mai wata uku kun san an kai mace bango ne."

Tace idan zata yi aure, sai ta tankade tare da rairaye wanda zata aura domin samun nagartaccen miji.

"Zan lura da komai da idon basira tun muna soyayya kafin aure. Ba nan kawai ba, zan duba irin gidan da ya fito, don wasu a tarbiyarsu babu kauna da tausayi kamar yadda ak tarbiyantar da yara nagari. Har da 'yan uwan namiji sai na duba da kyau kafin in yanke hukuncin iya auren shi."

Kara karanta wannan

Yadda na kama mijina da 'dandazon' mata a gadon aurenmu, Matar Aure tayi bayani a bidiyo

Duk da shekarunta 52, ta bayyana cewa tana da manema da yawa.

"Sai dai, ina taka-tsan-tsan saboda abinda na fuskanta a baya. Akwai wasu irin nagartattun halaye da nake son namiji ya mallaka wanda har yanzu ban samu mai irinsu ba. Ina son tabbacin halayen nan kafin in amince da auren mutum."

Yadda na kama mijina da 'dandazon' mata a gadon aurenmu, Matar Aure tayi bayani a bidiyo

A wani labari na daban, matar dake da muryar nan da 'yan kafar sada zumuntar zamani ke ta hawa wacce ke bayyana "dandazon mata cike da dakinta" ta bada labari a sabon bidiyo.

Idan za mu tuna, bidiyon ya yadu a cikin kwanakin nan inda take bayyana yadda mijin ta ya kwaso karuwai ya cika mata daki da su suna ta badala.

Duk da mutane sun ga cewa, matar tana bayanin ne a gaban kotu yayin da take korafi kan tsagwaron cin amana da neman mata irin na mijinta, sun dauka abun da nishadi.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ba zam huta ba har sai na samar da sassauci ga yan Najeriya, Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng