Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kai hari gidan ɗan takarar gwamnan Osun

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kai hari gidan ɗan takarar gwamnan Osun

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki gidan ɗan takarar gwamnan jihar Osun na jam'iyyar Labour Party (LP), Yusuf Lasun
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun buɗe wuta a gidan, babu wanda ya jikkata amma sun farfasa gilasan gidan
  • Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da harin, ya ce sun gode Allah babu wanda ya ji rauni

Osun - Da safiyar nan ta Litinin, wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari gidan Yusuf Lasun, ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party a zaɓen jihar Osun.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, farkon safiyar Litinin a gidan ɗan siyasar da ke Ilobu, ƙaramar hukumar Irepodun.

Kara karanta wannan

Kokarin ɗinke ɓarakar APC ya gamu da babban cikas, Jigo kuma shugaban kwamitin sulhu ya fice daga jam'iyyar

Rahotanni sun nuna cewa ba bu wanda ya jikkata yayin harin amma maharan sun yi wa gidan ɓarna yayin da suka buɗe wuta.

Barnar da maharan suka yi.
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun kai hari gidan ɗan takarar gwamnan Osun Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Harin da aka kai gidan Mista Lasun, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin tarayya, awanni bayan ya fafata a muhawarar 'yan takarar gwamna da ya gudana a Osogbo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wurin muhawarar, Yusuf Lasun, ya fuskanci gwamnan Osun na APC, Gboyega Oyetola, Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP, Oyegoke Omigbodun na jam'iyyar SDP da Akin Ogunbiyi na Accord Party.

Mista Lasun ya ɗora laifin rashin tsaro da ya addabi jihar da mafi yawan sassan Najeriya kan gwamnati kuma ya yi kira da a samar da yan sandan jihohi.

A ranar 16 watan Yuli, 2022, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC zata gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sojoji sun ragargaza kwamandojin Boko Haram, sun samo miyagun makamai

Bello Saheed, ɗan uwan Mista Lasun, ya shaida wa jaridar cewa:

"Ina tunanin hakan ta faru ne saboda muhawarar da aka gudanar jiya, saboda ana kammala wa labari ya canza a jihar Osun."
"Wannan ba shi ne karo na farko ba, an taɓa kai masa hari a kwanakin baya, an kai hari Ofishinsa watanni kaɗan da suka gabata kuma ko a wancan lokacin ba mu wani tada hankali ba saboda mutanen Osun sun san abinda ke faruwa."

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Mista Saheed ya ce 'yan bindiga sun buɗe wa gidan wuta ba ƙaƙƙautawa daga waje, inda suka farfasa gilasan tagogin gidan.

Ya ce dakarun 'yan sanda da jami'an tsaron jiha sun bazama neman maharam domin damƙe su da hukunta su, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da kai farmaki gidan Mista Lasun, "Da gaske ne, amma mun gode Allah ba bu wanda ya jikkata."

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Rikicin PDP ya tsananta, Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2023

A wani labarin kuma 'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyan N4.3bn na fansar Fasinjojin jirgin ƙasa

Yan ta'addan da suka farmaki jirgin kasan Kaduna-Abuja sun nemi a biya miliyan N100m kan kowane mutum ɗaya.

Bayan kubutar mutum 7 ranar Asabar, shugaban iyalan waɗan da aka sace, Abdulfatai Jimoh, ya ce ya zama saura Fasinjoji 43 hannun.

su

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262