Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, Ndume

Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza, Ndume

  • Senata Ali Ndume ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaro sun gaza a fannin tsaro
  • Ali Ndume ya misalta harin da yan bindiga suka kai gidan yarin kuje kamar shiga wurin shakatawa da fita cikin sauki
  • Ndume ya ce shugaba Buhari ya kamata ya rika yiwa al’ummar kasa bayani a irin wadannan lokuta ba hadiman sa ba

Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin soji, Ali Ndume, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar kan tabarbarewar tsaro a kasar. Rahoton Premium Times

Mista Ndume, dan majalisar dattawa na jam’iyyar APC mai wakiltar Borno ta Kudu, dangane da mummunan harin da aka kai gidan yarin Kuje a ranar Talata, ya ce shugabancin kasar ya gaza a babban kudirin sa na ga ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

Kamar yawo zuwa wurin shakatawa, haka kungiyar, ISWAP, ta kai mumunan hari gidan yarin Kuje da ke Abuja tare da sako fursunoni sama da 600 cikin sauki.

ndume
Harin gidan yarin Kuje: Buhari da shuwagabannin tsaro sun gaza wa – Ndume FOTO Premium Times
Asali: UGC

Duka ‘yan ta’addan Boko-Haram 64 da ke gidan yarin na daga cikin fursunonin da suka tsere a harin da ya yi sanadin mutuwar jami’in NSCDC tare da lalata dukiyoyin wurin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mista Ndume, a ranar Alhamis a wata hira da yayi a gidan talabijin na Channels, ya ce da harin ba zai yiwa yan ta’addan sauki ba inda gidan yarin ya kasance da isassun makamai da isassun ma’aikata.

"Na tabbata da jam’ian tsaro sun gaggauta kai dauki da an samu nasarar dakile harin amma sun dauki tsawon sa'o'i hudu a gidan yari babu taimako daga koina,” in ji Sanatan.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Senata Ndume ya koka da yadda gwamnati mai ci a yanzu ke sanya mutanen da ba su iya aiki ba shugabanci a wurare masu muhimmanci.

Da yake nuna goyon baya ga ‘yan Najeriya , Sanatan ya nuna rashin jin dadinsa da yadda masu magana da yawun shugaba Buhari ke fitar da jawabi iri daya a duk lokacin da irin wannan bala’i ya faru.

Ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya kasance mai yiwa al’ummar kasa bayani a irin wadannan lokuta, ba masu taimaka masa kan harkokin yada labarai ba.

Harin Kuje: ‘Allah ne kadai ya cece mu’ – Abba Kyari ya bada labarin abun da yafaru

Wani Labari, Bayan harin da yan bidigan kungiyar ISWAP suka kaiwa gidan yarin Kuje a daren ranar Talata ya lafa.

Dakataccen tsohon Mataimakin kwamshinan yansanda DCP Abba Kyari wanda fursuna ne a gidan yari ya ba da labarin abin da ya auku a ranar harin, Rahton jaridar VANGUARD.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa