Mutanen Legas na cin abincin Biliyan N4.5bn kowace rana, Gwamna Sanwo-Olu
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce mazauna jihar Legas na cinye abinci na kusan biliyan Huɗu da rabi a kowace rana ɗaya
- A cewar gwamnan jihar wacce ke gabar ruwa bata da yawan filaye a tsandaurin ƙasa amma akwai mutane miliyan 21 da ke rayuwa a ciki
- Ya ce jihar ke cinye naman shanu 50 cikin ɗari na wanda ake sarrafawa a faɗin kasar nan wanda ya kai na biliyoyi
Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce mazauna jihar na cin abincin da ya kai na Biliyan hudu da rabi kowace rana guda, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne a Legas jiya Litinin a wurin buɗe taron ƙara wa juna sani na shiyyar kudu maso yamma wanda a kai wa taken, "Aiwatar da sabbin tsarukan sarrafa abinci a Najeriya 2022."
'Ku bi umarnin Annabi SAW' An roki Malaman Addinin Musulunci a Najeriya kar su ruɗu da kuɗin yan siyasa
Ma'aikatar kuɗi, Kasafi da tsare-tsaren kasa tare da haɗin guiwar ma'aikatar noma ta jihar Legas da ma'aikatar tattalin arziki, tsare-tsare da kasafi ta Legas ne suka shirya taron na kwana biyu.
NAN ta rahoto cewa jihohin Legas, Oyo, Ogun, Ondo, Osun da Ekiti duk suna halartar taron yayin da jihar Legas ke zama mahaɗar jihohin shiyyar baki ɗaya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kwamishinan tattalin arziki, tsare-tsare da kasafi, Sam Egube, ya ce Legas ta yanke zata ja ragamar tabbatar da samar da abinci ga mutane masu banbancin hanyoyin noma da kiwo.
A cewarsa jihar Legas na da kyakkyawan tarihin haɓakar tattalin arziki da kuma samun canji mai kyau.
Daily Trust ta ruwaito Gwamnan na cewa:
"Jihar mu ke da kaso 60% na harkokin kasuwanci da masana'antu. Legas jiha ce dake a bakin ruwa, kuma hakan ya sanya take da ƙaranci filin ƙasa duk da kasancewarta gida ga mutane miliyan 21."
'Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗin kwalejin Ilimi
"Mazaunan jihar na lakume abincin kusan Biliyan N4,5bn a kowace rana guda da kuma kashi 50% na naman shanun da ake samarwa a kasar nan, wanda ke kaiwa na Biliyoyin kuɗi a wasu harkokin kasuwanci da cinikayya faɗin jihar."
A wani labarin kuma tattaunawar da ake domin haɗa kai tsakanin jam'iyyar NNPP ta Kwankwaso da LP ta Peter Obi ta rushe baki ɗaya
Tsohon shugaban jam'iyyar APGA, Victor Umeh, ya bayyana cewa tattaunawar haɗin guiwa tsakanin jam'iyyun LP da NNPP ta ƙare tun ranar 15 ga watan Yuni.
Umeh, wanda ke neman kujerar Sanata karkashin jam'iyyar LP ya ce tattaunawar, "Ta rushe baki ɗaya ," saboda kowane ɓangare ya ƙi yarda da wanda zai zama ɗan takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng