Sama da gidajen burodi 40 sun rufe shago a birnin Abuja
- Gidajen burodi da dama sun rufe shaguna saboda tsadar kayan aiki da kuma takurawar wasu hukumomin gwamnati
- Masu gidajen burodi da dama a Abuja sun rasa abin dogaro da kai, yayin da ma’aikata ke rasa aikin yi
- Shugaban Kamfanin Buredin Abuja na Master Bakers ya ce hukumomi gwamnati kamar NAFDAC, NESREA da SON ke kawo musu cikas
Abuja - Akalla gidajen burodi 40 ne suka rufe shaguna a babban birnin tarayya, Abuja, saboda tsadar kayan aiki, karin haraji da kuma karin kudin wutar lantarki da sauransu.
Wasu gidajen biredi da aka ziyarta ba su bude ba saboda tsadar kudin biyan masu aiki da yawan harajin da hukumomin gwamnati ke karba.
Wasu daga cikin gidajen burodin da suka rufe shago sun hada da Abumme bakery Ltd. Lugbe, dake kan Airports road, Hamdala Bakery a Kuje, Harmony Bite Baker a Karu, da kuma Doweey Delight Bakery Ltd, dake Kubwa kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta rawaito.
Sauran sun hada da Merit Baker, Mpape, Funez Baker, Orozo, Slyz Bakery, Wuse Zone 2, da sauransu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ishaq Abdulraheem, Shugaban Kamfanin Buredi na Abuja Master Bakers, FCT, ya bayyana cewa al’amarin ya zama abun tsoro ganin yadda gidajen burodin da ke Abuja basa su iya jure tsadar kayan aiki.
Ya ce akasarin masu gidajen burodi sun rasa abin dogaro da kai, yayin da ma’aikata suka rasa aikin yi saboda rufe wuraren aikin su.
Yayi kira ga gwamantin da ta gaggauta kawo musu dauki musamman ga hukumomin gwamnati dake kawo wa kasuwancin su cikas.
Ya bayyana wasu daga cikin hukumomin da suke kawo musu cikas sun hada da Hukumar Kula da Magungunan Abinci ta Kasa, NAFDAC, Standard Organisation of Nigeria, SON, National Environmental Standards and Regulations, da Hukumar NESREA.
Ya ce yawan haraji da kananan hukumomi shida dake Abuja suke karba ke sanya kasuwancin burodi yana wahala.
Limamin Katolika da aka yi garkuwa da shi ya samu 'yanci
A wani labarin kuwa, bisanin cika awanni 24 da sace shi, wani limamin cocin Katolika na Kaduna, Reveren Fada Emmanuel Silas, ya samu 'yanci daga hannun yan bindigan da suka yi garkuwa dashi kamar yadda jaridar LEADERSHIP ta rawaito.
Shugaban jam’iar cocin katolika na Kafanchan, Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da sakin Faston a ranar Talata a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Kaduna.
Asali: Legit.ng